Shugaba Tinubu Ya Gano Hanyar Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro da ta'addancin da ake fama da su a wasu jihohin Najeriya
- Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta shawo kan matsalar rashin tsaro ta hanyar gano bakin zaren tun daga tushe
- Shugaban kasan ya kuma yaba da jarumtar da dakarun sojoji suke nunawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tokyo, Japan - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana yadda gwamnatinsa za ta fuskanci matsalar ta’addanci da rashin tsaro.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta fuskanci ta'addanci ta hanyar magance tushen matsalar tare da ci gaba da dorawa a kan nasarorin da rundunonin tsaro na Najeriya suke samu a filin daga.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Laraba a wajen tattaunawa kan zaman lafiya da dorewar tsaro yayin taron Tokyo International Conference on African Development (TICAD9) a Yokohama, Japan.
Shugaba Tinubu ya yabawa sojoji
Shugaba Tinubu ya yaba wa sojoji bisa jajircewa da karfin guiwar da suke nunawa wajen kare Najeriya daga ta’addanci, ’yan bindiga da masu aikata laifuffuka, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ya ce sadaukarwar da dakarun suka yi ta kafa tubalin zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda gwamnatinsa ta kuduri aniyar karfafawa ta hanyar sauye-sauye, saka jari da kuma shugabancin damawa da kowa.
"Jaruman sojojinmu na iya lashe yake-yake da dama, amma za mu yi adalci ga jarumtaka da sadaukarwarsu ne kawai idan mu a matsayin gwamnati mun samu karfin gwiwa wajen magance ba wai ta’addanci kaɗai ba, har da tushen abubuwan da ke haifar da shi.”
- Shugaba Bola Tinubu
Ya jaddada cewa nasara ta dindindin a kan rashin tsaro na bulatar haɗa nasarorin sojoji da ingantattun sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arziki.

Source: Facebook
Wace hanya za a magance rashin tsaro
"Mun koyi cewa sojojinmu jarumai za su iya cin yaƙe-yaƙe da yawa. Amma za mu yi adalci ga jarumta da sadaukarwarsu ne kawai idan mu, a matsayin gwamnati, muka nuna ƙarfin hali wajen zama masu tsauri ba kawai a kan ta’addanci ba, har ma a kan abubuwan da ke haifar da ta’addanci."

Kara karanta wannan
"Sojoji ba za su iya murkushe yan bindiga a jihohi 7 ba," Gwamna ya tsage gaskiya
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya sake tabbatar da cewa haɗin kai, bambancin al’adu da bin doka, su ne babban karfin da Najeriya ke tunkaho da shi.
'Dan majalisa ya koka kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Malumfashi, Hon. Aminu Ibrahim, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a mazabarsa.
'Dan majalisar ya bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutane kusan 50 yayin wasu hare-hare da suka kai a kauyukan da ke mazabarsa.
Aminu Ibrahim ya bayyana cewa a wani daga harin da 'yan bindigan suka kai, sun kona mutane 20 bayan sun kai farmaki a kauyensu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
