Gwamnan Kano, Abba Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci

Gwamnan Kano, Abba Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Sa’idu Yahya a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano
  • Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kuma rantsar da saba bin masu ba da shawara guda uku da za su taimaka wa gwamnati a fannoni daban-daba
  • Gwamnan ya kara da gargaɗin sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa da ya guji son kai da cin hanci tare da yin aiki da gaskiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Sa’idu Yahya a matsayin sabon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Cin Hanci ta jihar.

An gudanar da rantsuwar ne a fadar gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba, karkashin jagorancin babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isah Dederi.

Kara karanta wannan

Kudin data, kira za su yi sauki, Tinubu ya dakatar da harajin 5% na kamfanonin sadarwa

Gwamnan Kano ya rantsar da sababbin hadimansa
Abba Kabir Yusuf yayin rantsar da shugaban PCACC da sauran hadimansa a Kano Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Hadimin gwamnan Kano, Ibrahim Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa cewa an nada Yahya ne bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya rantsar da sababbin mashawarta

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa baya ga sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci, Gwamna Abba ya kuma rantsar da sababbin masu ba shi shawara guda uku.

Sun haɗa da:

1. Kabiru Haruna Getso a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin samar da ayyukan yi.

2. Sale Musa Sa’adu a matsayin mai ba da shawara kan zamantakewa

3. Sylvester Kole a matsayin mai ba da shawara kan al’amuran al’ummar Kudu maso Kudu.

Jawabin Gwamnan Kano bayan rantsar da hadimansa

Da yake jawabi bayan rantsuwar, Gwamna Abba ya ce an zaɓi sababbin shugabannin ne bisa cancanta, inda ya bukace su da su tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi

Ya ja kunnen sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da ya guji nuna son kai yayin gudanar da aikinsa.

Abba Kabir Yusuf ya kuma jaddada cewa abin da ya kamaci sabon Shugaban shi ne aiki fisabilillahi ba don mutum ba.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamnan ya yaba wa tsohon shugaban hukumar, Muhyi Magaji, bisa jajircewar da ya nuna a lokacin shugabancinsa, tare da shawartar Sa'idu ya tuntuɓi magabacinsa idan akwai bukatar hakan.

Jawaban sababbin jami'an gwamnatin Kano

A nasa jawabin, sabon shugaban hukumar, Sa’idu Yahya, ya sha alwashin gudanar da aikinsa da kwazo kuma a kan doron adalci.

Shi ma a madadin sababbin masu ba da shawara, Kabiru Haruna Getso ya gode wa gwamna bisa damar da ya basu.

Ya kara da ba shi tabbatacin cewa za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen cika ayyukan da aka dora musu bisa gaskiya da amana.

Gwamnatin Kano ta yi sababbin naɗe-naɗe

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ƙara ƙarfafa gwamnatin sa da nadin sabbin mutane a muhimman mukamai daban-daban.

Kara karanta wannan

Rikici ya kacame da Shugaban karamar hukuma a Neja ya maka Gwamna Bago a kotu

Gwamnan ya ce naɗe-naɗen na daga cikin shirye-shiryen da gwamnatinsa ke ƙoƙarin inganta ayyukan gwamnati da tabbatar da ci gaba mai dore wa a lungu da saƙo na Kano.

Waɗanda su ka rabauta da muƙaman sun haɗa da Malam Haladu Mohammed, Muhammad Inuwa Jika da Ramadan Yusuf, kuma Gwamnan ya horé su da aiki tuƙuru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng