Kotu Ta Yi Belin Mutane 20 da Ake Zargi da Kisan Hausawa Mahalarta Aure a Plateau

Kotu Ta Yi Belin Mutane 20 da Ake Zargi da Kisan Hausawa Mahalarta Aure a Plateau

  • Babbar kotun Jihar Plateau ta yi zama kan shari'ar da ake bayan kisan matafiya a jihar wanda ya tayar da kayar baya
  • Kotun ta bayar da beli ga mutum 20 da ake zargi da kashe yan biki 13 a Mangu, bayan sauraron bayanan lauyoyinsu
  • Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume hudu ciki har da kisan kai da kuma mu'amala da makamai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Babbar kotun jihar Plateau ta ci gaba da zama game da shari'ar wasu da ake zargi da kisan kai.

Kotun ta bayar da belin mutane 20 da ake zargi da hannu a kisan mahalarta biki 13 a kauyen Mangu, karamar hukumar Mangu.

Kotu ta ba da belin wadanda suka kashe Hausawa a Plateau
Gwamna Caleb Mutfwang yayin wani taro a gidan gwamnati. Hoto: Calen Mutfwang.
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Mai shari’a Nafisa Lawal Musa ta bayar da belin ne bayan sauraron lauyoyinsu.

Kara karanta wannan

Dilolin kwaya 2 sun gamu da hukumar NDLEA, kotu ta yanke masu shekaru 10 a kurkuku

Harin da ya yi ajalin Hausawa a Plateau

An kai wa mutanen hari ranar 12 ga Yuni, 2025, a hanyarsu ta zuwa Qua’an Pan domin halartar bikin aure na wani dan uwansu.

‘Yan sanda sun gurfanar da mutanen a shari’a mai lamba PLD/115CR/2025, bisa tuhume-tuhume hudu ciki har da hadin baki da kisan kai da yin barna.

A cewar ‘yan sanda, laifuffukan sun sabawa sassan 59, 220, 313 da 189 na dokar jihar Plateau ta 2017, wadanda suka tanadi irin wadannan laifuffuka.

Kotu ta ba da belin wadanda da ake zargi

Lauyoyin da suke kare wadanda ake zargin Garba Pwul da I.S. Ikutanwa sun nemi beli a watan Yuli a gaban Mai shari’a Boniface Ngyong amma lokaci bai ba su damar samu ba.

Kotun ta ba su shawarar su sake gabatar da bukata a gaban alkalin, sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2025 domin cigaba.

Kara karanta wannan

Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari

Umurnin kotun da aka bayar ranar 14 ga Agusta, 2025, ya nuna cewa an gabatar da bukatar belin ranar 11 ga Agusta ta hannun lauyoyin.

Kotu ta yi zama a shari'ar da ake yi bayan kisan Hausawa a Plateau
Taswirar jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Rokon da lauyoyi suka yi wa kotu

Lauyoyin sun roki kotu ta yi la’akari da shawarar dakataccen lauya mai kare jama’a daga ofishin babban lauyan jihar Plateau kan batun.

Sun kuma bukaci kotu ta sallami wadanda ake tuhuma ba tare da wani sharadi ba, ko kuma ta bayar da belin har sai lokacin shari’a.

Bayan sauraron hujjojin, Mai shari’a Musa ya amince da bukatar lauyoyin, yana mai cewa matakin adalci ne kuma bai hana kotu ci gaba da shari’a ba.

Plateau: Tinubu ya umarci hukunta makasa Hausawa

Mun ba ku labarin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan kisan da aka yi wa ƴan ɗaurin aure a Plateau.

Tinubu ya bayyana kisan gillar a matsayin abin ƙyama wanda ba za a amince da shi ba ko kaɗan.

Shugaban ƙasar ya umarci hukumomin da su tabbatar da cewa sun zaƙulo masu hannu a harin da aka kai kan matafiyan da suka taso daga Kaduna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.