Katsina: Ana Batun Sulhu, Ƴan Bindiga Sun Illata Juna, Jagora da Miyagu 9 Sun Mutu
- Rikici ya barke tsakanin ‘yan bindiga a jihar Katsina inda suka yi bata kashi yayin da ake maganar sulhu a yankin Arewacin Najeriya
- Lamarin ya faru ne a Gidan Mai Aure a karamar hukumar Matazu da ke jihar Katsina a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Shaidu sun bayyana cewa kungiyar Saimaila ta Salihawa da ta Muhammadu daga Maharba sun yi arangama saboda rikicin iko
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Babban lamarin da ke kara kawo matsala yayin ake bukatar sulhu shi ne rigima tsakanin yan bindiga a Katsina.
Sabon rikicin da ya auku a jihar ya dauki sabon salo tsakanin ‘yan bindiga da kansu wanda ke kara ta'azzara matsalar.

Source: Original
An samu labari daga shafin Zagazola Makama cewa lamarin ya faru a daren Litinin 18 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rikicin zai iya shafar sulhu a Katsina
Wannan rigima ba shi ne karon farko ba da ake samu tsakanin manyan yan bindiga wanda ke ragewa jami'an tsaro aiki a yaki da ta'addanci.
Rigimar na zuwa ne yayin da wasu yankuna a jihar Katsina suka yi zama da yan bindiga domin yin sulhu da su saboda samun zaman lafiya.
Sai dai yawan rikici tsakanin yan bindigan zai iya kawo cikas ga ƙoƙarin tattaunawa da ake yi da su duba da tasirin da hadin kansu zai yi a sulhu.
A wasu yankuna Katsina zaman lafiya ya fara dawowa bayan sulhun da al’umma suka yi da ’yan bindiga ba tare da gwamnati ba.
Majiyoyi sun ce manoma sun koma gonaki cikin kwanciyar hankali, inda wasu suka ce shekaru da dama basu yi noma ba amma yanzu rayuwa ta sauya.

Source: Facebook
Yan bindiga sun hallaka junansu a Katsina
Majiyoyi suka ce abin da ya kamata ya kasance bikin suna cikin farin ciki ya zama tashin hankali da rasa rai.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa
Lamarin ya faru ne a Gidan Mai Aure kusa da kauyen Sayaya a karamar hukumar Matazu a Katsina.
Shaidu sun ce rikicin ya hada da kungiyar da Saimaila daga kauyen Salihawa ke jagoranta da kuma wata kungiyar Muhammadu daga kauyen Maharba.
Majiyoyi sun bayyana cewa ana samun gagarumin rashin jituwa tsakanin kungiyoyin saboda neman iko da filaye.
Rikicin ya barke ne lokacin da Muhammadu ya kai farmaki domin nuna iko kan abokin hamayyarsa.
Lokacin da aka kammala arangamar, an tabbatar da cewa Saimaila da wasu mabiyansa tara sun rasa rayukansu a wajen taron suna.
Irin wadannan rikice-rikicen kan nuna yadda kungiyoyin ‘yan bindiga ke kara rarrabuwa, suna gwabzawa kan hanyoyin fatauci, tara haraji da ribar kudin fansa.
Yan bindiga sun kai hari masallacin Katsina
A baya, kun ji cewa rahotanni sun bayyana yadda 'yan bindiga suka farmaki masallata a wani kauyen da ke garin Malumfashi a jihar Katsina.
Mutanen da suka tsira daga harin sun bayyana cewa suna cikin sallar Asuba kawai 'yan bindiga suka bude musu wuta.
Majiyoyi sun nuna cewa adadin mutanen da suka rasa ransu yayin harin ya hallaka mutum 30, sabanin mutane 13 da gwamnati ta ce sun rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
