Dilolin Kwaya 2 Sun Gamu da Hukumar NDLEA, Kotu Ta Yanke Masu Shekaru 10 a Kurkuku

Dilolin Kwaya 2 Sun Gamu da Hukumar NDLEA, Kotu Ta Yanke Masu Shekaru 10 a Kurkuku

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta samu nasarar cafke manyan dilalan miyagun ƙwayoyi biyu a Legas da Ogun
  • Kotun tarayya ta yanke musu hukuncin shekaru 10 a kurkuku tare da zabin biyan tarar miliyoyin Naira da wadanda aka kama da laifin
  • An kama musu kayan wiwi mai nauyin ton kusan uku da aka shirin rarrabawa sassan Najeriya don kara gurbata tarbiyyar matasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta samu nasara a kotu a kotu inda aka daure wasu manyan dilalan kwayoyi guda biyu da jihohin Legas da Ogun.

Mutanen da aka daure su ne Ajetsibo Emami mai shekaru 37 wanda aka fi sani da ‘Warri Kinsman’, da kuma Solomon Akpomuai mai shekaru 51.

Kara karanta wannan

Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari

NDLEA ta kama dilolin kwaya a Najeriya
Guda daga cikin dilolin kwaya da NDLEA ta kama da hajarsa Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Kotun tarayya da ke Legas ta yanke masu hukuncin shekara 10 a kurkuku baki ɗaya bayan an tabbatar da laifin safarar miyagun ƙwayoyi a kansu.

Yadda NDLEA ta kama dillalin kwaya

Jaridar ICIR ta ruwaito cewa nuna cewa jami’an NDLEA sun cafke Emami ne a Ikeja, Legas a ranar 28 ga Yuni, 2025 bayan sun kai wani samame na kwanaki uku yankin da ya ke.

An gano jakunkuna 24 makare da tabar wiwi mai nauyin kilo 414.2 bayan an samu sahihin bayanan leƙen asiri cewa Emami na ƙoƙarin fara raba haja.

Bayan gurfanar da shi a gaban Mai shari’a Deinde Dipeolu a kotun tarayya, an tuhume shi da aikata babban laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Alƙali ya yanke masa hukuncin shekara shida a gidan yari ko kuma biyan tara ta ₦50m don ya fanshi kansa daga daurin.

Kwastam ta damke karin dillalin kwaya

Kara karanta wannan

Alhaki ya kama su: 'Yan bindiga sun yi hadari bayan karbo makudan kudin fansa

A gefe guda, jami’an kwastam ne suka fara kama Solomon Akpomuai a kan babbar hanyar Shagamu-Ijebu-Ode a ranar 3 ga Yuni, 2025 da kaya mai nauyin kilo 2,197.8 na wiwi.

Daga bisani aka miƙa shi ga NDLEA a ranar 16 ga Yuni, inda aka gurfanar da shi a gaban kotun tarayya da ke karkashin Mai shari’a Dipeolu.

Solomon Akpomuai da NDLEA ta kama
Solomon Akpomuai a wani hoto da NDLEA ta dauka da ledojin wiwi Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Twitter

Kotu ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin shekara 4 a kurkuku ko kuma biyanshi ma ya biya tarar ₦50m.

NDLEA ta ce wannan nasara hujja ce cewa ba za ta yi sassauci ba wajen bin diddigin manyan masu fataucin ƙwayoyi da ke lalata matasa da kuma tattalin arzikin ƙasa.

Hukumar ta shawarci al’umma da su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci domin ci gaba da karya lagon masu safarar kwayoyi a Najeriya.

Hukumar NDLEA ta kai samame a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar NDLEA reshen jihar Kano, ta bayyana cewa ta sami nasarar cafke mutanen da ake zargin da laifuffukan fataucin miyagun ƙwayoyi.

Sadiq Muhammad-Maigatari, jami’in hulɗa da jama’a na NDLEA ta Kano, ya sanar da wannan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 13 ga Agusta, 2025, inda ya ce an samu nasara.

Samamen ya gudana ne a ranakun 7 da 8 ga watan Agusta a wurare da aka sani da harkokin miyagun ƙwayoyi a Kano—kamar Massallacin Idi, Fagge Plaza, Kofar Mata da Kofar Wambai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng