Borno, Kaduna, Zamfara da Jihohin Arewa 16 da Za Su Samu Ruwan Sama Ranar Laraba

Borno, Kaduna, Zamfara da Jihohin Arewa 16 da Za Su Samu Ruwan Sama Ranar Laraba

  • NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da iska hade da tsawa a wasu jihohin Arewa da Kudancin Najeriya ranar Laraba
  • Jihohin Arewa 16 da ake sa ran za su samu ruwan sama mai yawa a ranar Laraba sun hada da Kaduna, Taraba, Bauchi, Adamawa
  • NiMet ta shawarci jama’a da su guji tuki yayin ruwan sama, sannan an shawarci hukumomi su shirya kai dauki idan an samu ambaliya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Yayin da aka shiga rana ta 20 a cikin watan ruwa na Agusta, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama zai sauka a wasu jihohin Najeriya.

Hasashen NiMet ya nuna cewa ba za a samu ambaliyar ruwa a kowace jiha ba, amma dai za a samu ruwa da iska hade da tsawa a wasu sassan kasar.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sheka ruwan sama mai yawa a Kaduna, Neja da jihohin Arewa 13 ranar Talata

Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama a jihohin Arewa 19 a ranar Laraba
Ruwan sama da iska mai karfi na sauka a wasu sassan Najeriya. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

NiMet ta fitar da rahoton hasashen yanayi na ranar Laraba, 20 ga Agusta, 2025 a shafinta na X, inda ta yi bayani kan yanayin jihohin Arewa da Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen yanayi a jihohin Arewa

A jihohin Arewa, hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama hade da iska da tsawa a wasu yankuna na jihohin Borno, Taraba, Bauchi, Adamawa, Kaduna, da Gombe a safiyar Laraba.

Da yammaci har zuwa dare kuwa, NiMet ta ce za a ci gaba da samun ruwa da tsawa hade da iska a wasu sassan Arewa.

Jihohin da za su ci gaba da samun ruwan su ne; Kano, Jigawa, Borno, Zamfara, Yobe, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Bauchi, da Gombe.

Hasashen yanayi a Arewa ta Tsakiya

A shiyyar Arewa ta Tsakiya, rahoton hasashen NiMet ya nuna cewa za a samu ruwa mai matsakaicin karfi amma hade da iska da tsawa a Abuja da jihohin Nasarawa, Plateau, da Niger.

Kara karanta wannan

Daga Lahadi: Ruwan sama na kwana 3 zai jawo ambaliya a Gombe da jihohin Arewa 7

Za a kuma samu ruwa mai matsakaicin karfi amma hade da tsawa da iska a yammacin ranar a Abuja da jihohin Nasarawa, Niger, Plateau, Benue, Kwara da Kogi.

Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya

A Kudancin Najeriya kuwa, hukumar NiMet ta ce za a iya samun ruwan sama mai matsakaicin karfi a wasu sassan jihar Cross River kadai.

Amma a yammaci zuwa dare kuwa, za a iya samun ruwan sama a jihohin Ogun, Osun, Ebonyi, Delta, Lagos, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom.

NiMet ta ce ruwan sama hade da iska da tsawa za su sauka a sassan Najeriya ranar Laraba
Ruwan sama mai karfi da tsawa na sauka a wasu sassan Najeriya. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

Shawarwarin hukumar NiMet ga 'yan Najeriya

NiMet ta shawarci jama'a da su ci gaba da yin taka tsantsan game da yiwuwar ambaliyar ruwa, iska mai ƙarfi, da kuma katsewar al'amuran yau da kullun.

An kuma shawarci direbobi su guji tuki yayin ruwan sama mai yawa don kaucewa haɗurra sannan kada a fake a karkashin bishiyoyi yayin guguwa don gujewa fadowar reshe.

Hukumar ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayi na filin jirgin kafin tsara zirga-zirgarsu.

Karanta rahoton NiMet a nan kasa:

An nemi mutane su fito Sallar rokon ruwa

Kara karanta wannan

Kebbi, Neja za su fuskanci ambaliya, NiMet ta yi hasashen ruwa mai yawa a Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, malaman Musulunci a Kano sun bukaci ɗaukacin al'umma su fita sallar rokon ruwa sakamakon ƙarancin ruwan da ake fama da shi.

Shugaban Majalisar malamai ta Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu.

Sheikh Ibrahim Khaleel ya buƙaci musulmi su fito sallar rokon ruwa gobe Asabar da misalin ƙarfe 9:00 domin neman taimakon Allah a daminar bana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com