N70,000: Amurka Ta Koka da Karin Albashi, Matsalolin Shari'a da Tsaro a Najeriya

N70,000: Amurka Ta Koka da Karin Albashi, Matsalolin Shari'a da Tsaro a Najeriya

  • Amurka ta fitar da rahoton da ya nuna damuwa kan tsaro da kuma yadda ake gudanar da shari’a a Najeriya, musamman zargin tsare mutane ba tare da hukunci ba
  • Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ana ɗaukar matakai wajen gyara tsarin shari’a, ƙarfafa tsaro da kuma gyara tattalin arziki don rage matsin rayuwa
  • Rahoton ya kuma bayyana cewa sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da Bola Tinubu ya yarda da shi ba zai wadatar ba saboda raguwar darajar Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Amurka ta bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da harkokin tsaro da kuma tsarin shari’a a Najeriya.

Kasar ta ce akwai matsalolin tsare mutane ba tare da shari'a ba da kuma tsawaita shari’u ba tare da hukunci ba.

Kara karanta wannan

'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa fadar Shugaban Ƙasa ta yi martani da cewa gwamnati na aiwatar da sauye-sauye domin tabbatar da adalci, rage tsawaita shari’u da kuma kawo gyara a fannin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton na Amurka ya kuma yi tsokaci kan sabon mafi ƙarancin albashin N70,000, yana mai cewa raguwar darajar Naira ya rage fa'idar karin albashin.

Rahoton Amurka kan tsaro da shari’a

Rahoton da Amurka ta fitar ya bayyana cewa har yanzu akwai mutane da dama da aka tsare tun lokacin soke rundunar SARS a 2020, ba tare da sanin inda suke ba.

An ce jami’an tsaro na amfani da damar tsare mutane ba tare da takardar izini ba, kuma galibi suna tauye damar samun lauyoyi da ganin ‘yan uwa.

An kuma bayyana cewa wasu shari’u kan ɗauki shekaru kafin yanke hukunci saboda ƙarancin alkalai, cin hanci, jinkirin aiki da kuma tsoma bakin 'yan siyasa.

Kara karanta wannan

Mamakon ruwan ya lalata gidaje, ya raba mutane sama da 600 da muhallansu a Yobe

Maganar Amurka kan albashi da tattalin arziki

Rahoton ya bayyana cewa duk da ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N70,000, raguwar darajar Naira ya sa kudin ya riga ya rasa daraja.

Jaridar Punch ta wallafa cewa rahoton ya ce wasu daga cikin ma'aikatan Najeriya ba su samu karin albashin ba.

Shugaban kwadago, Joe Ajaero yayin zanga zangar neman karin albashi
Shugaban kwadago, Joe Ajaero yayin zanga zangar neman karin albashi. Hoto: Nigeria Labour Congress
Source: Facebook

Martanin fadar shugaban ƙasa ga Amurka

Hadimin Shugaban Ƙasa, Sunday Dare, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na ɗaukar matakai wajen inganta tsarin shari’a da rage tsawaita shari’u.

Ya ƙara da cewa akwai cikakken haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, abin da ya taimaka wajen rage matsalolin tsaro a cikin ƙasar.

Dare ya ce gyaran tattali da gwamnati ke aiwatarwa ya fara samar da sakamako, inda ya kawo misali da yabon da Amurka ta yi nasarar kama shugabannin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru.

Legit ta tattauna da malamin makaranta

Wani malamin makaranta a jihar Gombe, Hamza Adamu ya zantawa Legit Hausa cewa ba ƙarin albashi ba ne babbar damuwar ma'aikata a yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta biya wa Kiristoci rabin kudin kujerar ziyara zuwa Isra'ila

Malamin ya ce:

"Babbar matsalar ita ce darajar kudin da yadda za a saye abu da su. Ko da N10,000 za a biya, idan za ta biya bukata ai ba matsala."
"Ya kamata a dawo da darajar kuɗin mu, hakan zai fi karin albashi amfani."

Najeriya ta yi wa Amurka martanin batun biza

A wani rahoton, kun ji cewa ofishin harkokin wajen Najeriya ya yi magana kan sabuwar dokar biza da Amurka ta sanya wa 'yan Najeriya.

Najeriya ta bayyana cewa za ta yi nazari domin daukar irin matakin da Amurka ta dauka game da 'yan kasarta.

A makon da ya wuce ne Amurka da sanya sharadin bayar da bayanan kafafen sada zumuntan masu neman shiga kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng