Daga zuwa Umrah, Hukumomin Saudi Sun Cafke 'Yar Kano bayan Alakanta Jakarta da Wiwi
- Hukumomin Saudiyya sun cafke Maryam Hussaini Abdullahi, ‘yar Kano, bisa zargin da ya shafi wata jaka da aka ce tana ɗauke da tabar wiwi
- Abdullahi Baffa ya zargi Ethiopian Airlines da sauya jakunkunan da ya jawo aka danganta sunan matarsa da jakar da ba ta san komai a kan ta ba
- Ya roƙi gwamnatin Najeriya ta taimaka wajen tabbatar da gaskiya, ciki har da buƙatar a duba bidiyon CCTV a filin jirgin Kano don wanke mai dakinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumomin a kasar Saudiyya sun tsare wata ‘yar Najeriya mai suna Maryam Hussaini-Abdullahi, mai shekaru 39 daga jihar Kano.
Lamarin ya biyo bayan da aka danganta sunanta da wata jaka cike da tabar wiwi a filin jirgin sama na Jeddah.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Maryam, ta je ƙasar Saudiyya tare da mijinta, Abdullahi Baffa, a ranar 6 ga watan Agusta domin yin Umrah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai tafiyar ta su ta ibada ta rikide zuwa tashin hankali. bayan da jami’an tsaron Saudiyya suka ce sun gano sunanta a wata jaka da ake zargin tana cike da wiwi.
'Yar Najeriya ta samu matsala a Saudiyya
Daily Post ta wallafa cewa Abdullai Baffa ya zargi Ethiopian Airlines da haddasa matsalar, inda ya ce kamfanin ya haɗa sunan matarsa da jakar da ba ta san komai akanta ba.
A cewarsa:
“Matata ba ta da laifi. Mun tashi daga Kano da kowa da jaka daya, kuma duk an sanya musu alamar da ta dace. Lokacin da mu ka sauka a Jeddah, ba mu ga jakunkunanmu ba. Bayan wani lokaci sai kamfanin ya ce ya samo guda ɗaya, amma muna buƙatar mu karɓa a Jeddah. Mun ƙi, muka nemi a dawo da ita Kano.”
Bayan sun jira tsawon kwanaki ba tare da labarin kayansu ba, sai ma’auratan suka sayi sababbin kaya a Madina.
Amma al’amura suka ƙara rikicewa ne a lokacin da za su dawo gida makon da ya gabata, inda aka tsare Maryam, yayin da mijinta ya samu damar wucewa.
Ana binciken 'yar Najeriya a Saudiyya
Rahotanni sun nuna cewa an kai Maryam wata cibiya a Makka, inda aka tuhume ta a gaban jami’an ofishin jakadancin Najeriya.
Duk da cewa nambar alamar jaka ba ta yi daidai da na Kano ba, sai dai aka tsare ta domin bincike.

Source: Original
Mijinta ya jaddada cewa:
“Ta yi kuka lokacin da suka nuna mata jakar. Ba ta taɓa ganin ta ba. Ina ganin Ethiopian Airlines da jami’an filin jirgi sun san gaskiya amma suna boye ta.”
Baffa ya roƙi gwamnatin Najeriya ta sa baki cikin lamarin tare da buƙatar a saki bidiyon CCTV na filin jirgin sama na Kano don tabbatar da gaskiyar matarsa.
A halin yanzu, jami’in Ethiopian Airlines ya tabbatar da cewa ana bincike amma aikin zai ɗauki lokaci saboda ya shafi tashoshi da dama.
An kama wasu za su Saudiyya da kwaya
A baya, kun ji cewa Hukumar, NDLEA, ta sanar da kama wasu mutane da ke ƙoƙarin amfani da tafiya aikin Hajji a matsayin hanyar safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar Saudiyya.
A shekarar nan, hukumar ta NDLEA ta ce ta samu nasarar cafke shugabannin ƙungiyoyi uku da ke da hannu wajen tsara safarar ƙwayoyi daga Najeriya zuwa kasa mai tsarki.
A cewar hukumar, an kama wasu daga cikin mutanen ne a ranar 26 ga Mayu, 2025 a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, yayin da suke shirin hawa jirgin zuwa Jeddah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


