'Dan Majalisar Nasarawa Ya Fadi Dalilin Nada Hadimai sama da 100
- Dan majalisa a jihar Nasarawa, Musa Gude, ya nada masu taimaka masa sama da 100 a kokarin da ce yana yi domin habaka dimokuradiyya
- Ya bayyana cewa nadin zai inganta rayuwar mazauna yankinsa da iyalansu kuma ya nuna burinsa na tafiya da matasa a tsarin siyasa
- Gude ya ce ba wannan ne kawai aikin da ya yi ba, har ma ya gina rijiyoyi, ya biya kuɗin jarrabawar WAEC, tare da sama wa jama'a sana’o’i
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Nasarawa – Musa Gude, ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar mazabar Uke/Karshi, Musa Gude ya bayyana cewa ya nada hadimai 106 daga yankinsa.
Gude, wanda 'yan yankinsa su ka zabe shi a inuwa jam’iyyar SDP, ya bayyana cewa ya dauki matakin domin su taimaka masa wajen gudanar da wakilcin mutanen da su ka zabe shi.

Kara karanta wannan
Otedola: Yadda attajiri a Najeriya ya gagara yin makaranta, ya fadi yadda ya maimaita aji

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cewarsa, daga cikin nadin da ya yi akwai na musamman da na sirri, kuma manufarsa ita ce a inganta rayuwar waɗannan mutane da iyalansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan majalisar Nasarawa ya yi nade nade
Jaridar The Cable ta wallafa cewa 'dan Majalisa mai wakiltar Uke/Karshi a Nasarawa ya ce za a rika biyan hadimansa albashi a matakai.
Ya ce akwai wadanda za a biya albashin N100,000 yayin da wadansu za su rika karbar N10,000 a kowane karshen wata.
A kalamansa:
“Ina son in bayyana cewa ina da masu taimaka mani 106 a kan albashina, ciki har da na musamman da na sirri. Wasu daga cikinsu suna karɓar N100,000, N80,000, N50,000, N30,000, N20,000 da N10,000."
Gude ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na manufarsa ta jagoranci na haɗin kai da inganta rayuwar jama’a a mazabar sa.
Gude ya ce yana aiki a Majalisar Nasarawa
Musa Gude ya ƙara da cewa ya riga ya gina rijiyoyi da dama da kuma biyan kuɗin jarabawar WAEC ga ɗalibai da dama a yankinsa a matsayin wasu daga cikin ayyukansa.

Source: Original
Ya ce:
“Na yi iya ƙoƙarina a fannoni daban-daban kamar lafiya, ilimi, noma, ababen more rayuwa da sauransu. Haka kuma na ƙarfafa wa mutane da dama domin su dogara da kansu."
'Dan majalisar ya tabbatar wa al’ummarsa cewa zai ci gaba da samar da wakilci mai na gari a majalisar jihar domin kai masu ayyukan saukaka rayuwa.
Haka kuma ya yi kira ga mazauna mazabar da su zauna lafiya da haƙuri da juna, duk da bambancin da ke tsakaninsu.
Wani 'Dan majalisa ya nada hadimai 50
A baya, kun samu labarin cewa wani dan majalisar wakilai daga jihar Akwa Ibom, Emmanuel Ukpong-Udo, ya nada hadimai 50 domin taimaka masa wajen gudanar da ayyuka a Abuja da mazabarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan mataki ya zama abin tarihi a jihar wacce take fuskantar matsanancin rashin aikin yi duk da arzikin man fetur da take da shi kuma ake mora a kasa,
Sai dai dokar majalisar ta tanadi cewa kowane dan majalisa na iya daukar hadimai biyar kacal. Saboda haka, sauran 45 da ya nada daga aljihunsa zai rika biyansu albashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
