Dankari: Wani dan majalisar wakilai ya nada wa kansa hadimai 50

Dankari: Wani dan majalisar wakilai ya nada wa kansa hadimai 50

-Emmanuel Ukpong-Udo mai wakiltar Ikono/Ini a Majalisar wakilai ta tarayya ya kafa tarihi inda ya nada hadimai har mutum 50

-A dokar majalisar mutane biyar kacal aka yadda kowane mamba ya nada

-Daya daga cikin hadiman ya bayyana farin cikinsa da wannan nadin inda yace mamba nasu yayi hakan domin karfafa jama'ar yankin da ya fito

Wani dan majalisar wakilai mai suna Emmanuel Ukpong-Udo dan asalin jihar Akwa ibom ya nada hadimai guda 50 domin taya shi yin aiki.

Jihar Akwa Ibom na daya daga cikin jihohin Najeriya dake fama da rashin aikin yi duk da cewa ta na da arzikin man fetur. A don haka daukar hadimai guda 50 ga mutum daya ya zama tamkar kafa tarihi ne a Jihar.

KU KARANTA:Zaben Gwamna: APC zata gudanar da zaben fidda gwani a jihohin Bayelsa da Kogi ranar 29 ga watan Agusta

Mista Ukpong-Udo dan jam’iyyar PDP na wakiltar gundumar Ikono/Ini a Majalsar wakilai ta tarayya dake Abuja. Karonsa na farko kenan da shiga majalisar.

Dan majalisar ya rarraba muqamai da dama kama daga, mai taimaka masa kan ayyuka na musamman, kan hulda da jama’a, kan cigaban al’umma da kuma na lamurran mata.

Bugu da kari, dokar majalisar ta su, ta ba wa ko wane mamba damar daukan hadimai biyar ne kacal. A sakamakon haka sauran arba’in da biyar din da ya nada daga cikin aljihunsa zai rika biyansu albashinsu.

Dayan daga cikin hadiman wanda ya samu zantawa da jaridar Premium Times, Imowo Mbede ya ce, daukar mutane masu yawa a matsyin hadimai da dan majalisar yayi shi ne hanyarsa na karfafa jama’arsa.

Mista Mbede ya cigaba da cewa: “ Tabbas wannan hanya ce ta samar da aikin yi, akasarin mutanen da Mista Ukpong-Udo ya ba wa muqamai ‘yan yankin da ya fito ne wanda ya kunshi kananan hukumomi guda biyu kacal wato Ikono da Ini.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel