EFCC ta Kama Manyan Jami'an Hukumar NAHCON kan Zargin Badakala a Hajjin 2025
- Hukumar EFCC ta tsare manyan jami’an hukumar Alhazai ta kasa bisa zargin almundahana da ta shafi aikin Hajjin shekarar bara
- Rahotanni sun bayyana cewa an tsare jami'an ne da ake zargin ne saboda sun ki mayar da kuɗin da ake tuhumar su da dauka
- NAHCON ta ce tana maraba da hada kai da hukumar yaki da cin hanci, tana mai jaddada cewa ba za ta kare wanda aka samu da laifi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, wato EFCC, ta tsare wasu manyan jami’an hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) bisa zargin almundahana da ta shafi aikin Hajjin 2025.
Rahotanni daga majiyoyin cikin EFCC sun tabbatar da cewa jami’an biyu da aka kama suna tsare a hannun hukumar tun kwanakin baya.

Kara karanta wannan
Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari

Source: Facebook
Rahoton Punch ya bayyana cewa duk da haka, an ce ba a bayyana adadin kuɗin da ake tuhumarsu da dauka ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai a sakon da ta wallafa a X, hukumar NAHCON ta bayyana cewa tana maraba da bincike tare da hukumomin gwamnati masu alaka da yaki da cin hanci.
EFCC ta tabbatar da tsare jami'an NAHCON
Majiyoyin cikin hukumar EFCC sun tabbatar da cewa jami’an biyu suna tsare domin bincike kan zargin almundahana da suka shafi kuɗin aikin Hajjin 2025.
An ruwaito cewa hukumar ta bukaci jami’an da su dawo da kuɗin da ake zargin sun amsa, amma suka ki yin hakan, abin da ya sa aka ci gaba da tsare su.
Wani jami’in EFCC ya shaida cewa:
“Mun ce su dawo da kuɗin da suka dauka, amma sun ki yin hakan, shi ya sa muke ci gaba da tsare su.”
Matsayin hukumar NAHCON kan zargin
Jami'ar yada labaran NAHCON, Fatima Usara ta fitar da sanarwa a madadin shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, tana cewa ba za su boye wa hukumomin gwamnati komai ba.
A cikin sanarwar, hukumar ta ce tana bin ka’ida da gaskiya a duk ayyukanta tare da tabbatar da cewa tana ba da hadin kai ga hukumomin gwamnati, musamman masu yaki da cin hanci.
Sanarwar ta kara da cewa hukumar ba za ta boye duk wani jami’i da aka samu da laifi ba, domin tsaron amana da martaba.

Source: Twitter
NAHCON da kiran kaucewa yada jita jita
Hukumar NAHCON ta kuma yi kira ga jama’a da kafafen watsa labarai da su guji yada jita-jita kan lamarin.
Ta ce wajibi ne a bari hukumomi su kammala bincikensu bisa ka’idojin da aka kafa, domin kada a yi wa wadanda ake zargi hukunci a kafafen labarai kafin a tabbatar da gaskiya.
NAHCON ta jaddada cewa tana maida hankali kan kammala nazari bayan aikin hajjin bana tare da daukar matakan gyara domin kara inganta shirye-shiryenta.
EFCC ta tono dabarun 'yan siyasa na sata
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta koka kan yadda wasu 'yan siyasa suka bullo da dabarun sata kafin shiga ofis.

Kara karanta wannan
'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi
Hukumar ta bayyana cewa wasu 'yan siyasa na bayyana kadarorin da ba su mallaka ba domin toshe kofar gano satar da za su yi a ofis.
EFCC ta tabbatar da cewa za ta cigaba da daukar matakan da suka da ce domin yaki da cin hanci da rashawa a fadin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
