Fitaccen Malamin Musulunci Ya Yi Magana da Bello Turji Ta Wayar Tarho
- Fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Sakkwato, Sheikh Murtala Bello Asada ya tattauna da Bello Turji ta wayar tarho
- Wannan na zuwa ne yayin da ake yada rahotannin cewa kasurgumin dan bindigar ya shirya mika duka makamansa don a zauna lafiya
- Sheikh Asada ya yi magana da Turji ne domin tabbatar da aniyarsa ta neman zaman lafiya kuma sun yi hira mai tsayi kan hakan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Kasurgumin dan bindigar nan da ya addabi jihohin Arewa maso Yamma, Bello Turji ya tabbatar da cewa a shirye yake ya mika makamansa domin samun zaman lafiya.
Bello Turji ya tabbatar da shirinsa na rungumar zaman lafiya ne a wata hira da ya yi da fitaccen malamin nan, Sheikh Murtala Bello Asada ta wayar tarho.

Source: Facebook
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da hakan a wani sautin murya ya wallafa a shafinsa na X yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello Turji ya tabbatar da zai ajiye makamai
'Dan bindigar ya tabbatar wa malamin cewa a shirye yake ya mika makamansa matukar za a barsu su zauna lafiya.
Wannan dai na zuwa ne bayan rahotannin da suka fito kwanakin baya cewa an fara tattaunawar sulhu da Bello Turji da yaransa don dawo da zaman lafiya a Sakkwato, Zamfara da sauran jihohin Arewa.
A hirar da suka yi mai tsawon mintuna uku da wasu yan dakiku, Sheikh Murtala Bello Asada ya bukaci jin ta bakin Turji kan batun da ake yadawa cewa yana so a yi sulhu.
Malamin ya gargadi dan bindigar cewa maganar sulhu abu ne mai girma kuma ba za su so yaudara ba kamar yadda aka yi a baya.

Kara karanta wannan
Dalilin da yasa malaman addini suke sukar Assadus Sunnah kan haduwa da Bello Turji
Ya bukaci Turji da ya mika duka makamansa mutane su gani su tabbatar wannan karon dagaske ya rungumi zaman lafiya sabanin yaudarar da aka masu baya.
Abin da Sheikh Asada ya tattauna da Turji ta waya
Sheikh Asada: "Ina jin maganganu kuma ka san magana daga bakin mai ita tafi dadi, an ce kana son ka ajiye makamai, ina son naji gaskiyar maganar."
Bello Turji: "Haka ne malam,"
Sheikh Asada: "Za ka ajiye makaman dagaske?"
Bello Turji: "In sha Allahu malam, idan za a barmu mu zauna lafiya."
Sheikh Asada: "Ai wannan zama za a yi a yi sulhu, matsalar da ke akwai ita ce yaudara, kun yi ta cewa an yi sulhu da ku ana sabawa, kuma kun yi kuma kun saba."
Bello Turji: "Eh hakane amma kafin mu saba sai an saba mana."
Sheikh Asada: "Yana da kyau mutane su san cewa kada sai duniya ta dauki ka yi sulhu kuma daga baya ya zo ba haka ba. Amma yanzu maganar ta watsu sosai cewa za ka ajiye makamai.

Kara karanta wannan
Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu
Bello Turji: "In Sha Allahu."
Sheikh Asada: "Yanzu akwai wani lokaci da ka sanya na yin hakan?"
Bello Turji: "Gaskiya ban tsaida ba tukunna. Amma na kudurta ga zucciyata."
Sheikh Asada: "To don Allah ka ji tsoron Allah, ka dauka an samu jarabawa kuma idan aka koma ga Allah komai zai wuce, ka sa ma zuciyarka cewa za ka tuba don Allah ba dan wani ba, kuma wallahi idan ka yi haka Allah zai maka abin da baka tsammani.
A karshe, Malamin ya bukaci Bello Turji ya sanya mutanen da ya aminta da su, wadanda ba za su cuce shi ba domin mika makamansa ga gwamnati, yana mai cewa haka ne kadai zai sa mutane su yarda
Ga cikakiyar hirar da suka yi a nan:
Bello Turji ya fara daukar matakan sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa Bello Turji ya amince da dakatar da kai hare-hare kan manoma tare da sakin mutane 32 da ya yi garkuwa da su a dajin Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa ya yi hakan ne bayan ganawar sulhu da wasu malaman Musuluncina dajin Fakai da ke ƙaramar hukumar Shinkafi.
Sheikh Musa Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan, ya ce sun gana da Turji da wasu abokansa kamar Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila, inda duk suka amince da shirin zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

