'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci, Mutane da Dama Sun Rasu ana Sallah

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci, Mutane da Dama Sun Rasu ana Sallah

  • Yan bindiga sun kashe mutane akalla 13 su na tsakiyar sallar Asubah a kauyen Unguwan Mantau da ke yankin Malumfashi a Katsina
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dr. Nasir Mu'azu ya bayyana harin a matsayin na ramuwar gayya
  • Ya ce kwanaki biyu da suka wuce mazauna kauyen suka yi wa yan bindiga kwantan bauna, suka kashe da dama suka ceto yan uwansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Rahotanni daga jihar Katsina sun nuna cewa yan bindiga sun kai mummunan hari kan mutane ana tsaka da sallar Subahi a Unguwan Mantau da ke karamar hukumar Malumfashi.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata, 19 ga watan Agusta, 2025 lokacin da yan bindigar suka kutsa masallacin kauyen, suka bude wa masallata wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

"Sun mamaye mazabata": Dan majalisa ya fashe da kuka kan hare haren 'yan bindiga

Tasiwrar jihar Katsina.
Hoto taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin ta hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mazauna kauyen suka kashe yan bindiga

Dr. Nasir Mu’azu, cikin wata sanarwa, ya bayyana harin a matsayin “na ramuwar gayya da miyagu suka kaddamar” bayan mazauna kauyen sun yi wa ’yan bindiga kwanton bauna.

“Kwanaki biyu da suka gabata, mutanen Unguwan Mantau sun yi wa ’yan ta’adda kwanton bauna, inda suka kashe da dama daga cikinsu, suka ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Ruwan Sanyi.
"Sannan mutanen kauyen suka kwato babura uku da bindigogi AK-47 guda biyu,” inji kwamishinan.

Wane mataki aka dauka bayan harin masallacin?

Nasir Mu’azu ya ce tuni gwamnati ta yi gaggawar tura jami’an tsaro zuwa yankin bayan abin da ya faru a masallaci, rahoton jaridar Gazette Nigeria.

“Dakarun sojojin sansanin FOB da kuma ’yan sanda sun isa kauyen don bin sawun waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi.

Kara karanta wannan

Alhaki ya kama su: 'Yan bindiga sun yi hadari bayan karbo makudan kudin fansa

"A lokacin damina, waɗannan ’yan ta’adda na ɓoyewa a cikin amfanin gona su na kai hare-hare, amma mun kuduri aniyar cafke su da gurfanar da su,” in ji shi.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Hoton gwamnan Katsina a wurin kaddamar da rundunar CWC da ya kirkiro Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Gwamnatin Katsina ta yabawa Unguwan Mantau

Yayin da yake yabawa jarumtakar al’ummar garin, kwamishinan ya tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatin Dikko Radda ga mazauna Unguwan Mantau.

“Muna girmama jarumtar mutanen Unguwan Mantau tare da sake jaddada kudirinmu na kare dukkan rayukan jama'a a fadin jihar Katsina.
“Gwamnatin Jihar Katsina na tare da waɗanda sabon harin yan bindiga ya shafa a wannan lokaci mai wahala. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba sai da an dawo da cikakken zaman lafiya,” in ji Nasir Mu’azu.

Yan sanda sun ceto matafiya a Kasina

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun yan sanda sun yi nasarar dakile yunkurin yan bindiga na sace mutane a titin Funtu zuwa Gusau a Katsina.

'Yan sandan sun kuma ceto wasu mutane uku ba tare da wani rauni ba a Marabar Bangori da ke kan titin wanda ya yi kaurin suna wajen hare-haren yan bindiga.

Jami'an tsaron dai sun samu wannan nasarar ne bayan samun rahoton cewa 'yan bindiga sun tare wasu matafiya da ke kan hanyar zuwa Gusau, kuma suka kai daukim gaggawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262