Abubuwan 'Tashin Hankali' da Aka Gano a Hannun Mutane 333 da Aka Kama a Zaben Kano

Abubuwan 'Tashin Hankali' da Aka Gano a Hannun Mutane 333 da Aka Kama a Zaben Kano

  • Rundunar yan sanda ta gurfanar da mutane 333 da aka kama bisa zargin tada hargitsi a zaben cike gurbin da aka yi a Kano
  • Kwamishinan yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake tuhuma
  • Daga cikin abubuwan da aka karbe a hannun wadanda ake zargin akwai bindigogi, kudi, wukake, adduna da motoci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta tabbatar da cafke mutum 333 da ake zargi da hannu a yunkurin tada zaune tsaye a zaɓen cike gurbin yan majalisar jiha guda biyu ranar Asabar.

A ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, hukumar INEC ta gudanar da zaben cike gurbi a mazabun Ghari/Tsanyawa da Bagwai/Shanono.

Kwamishinan yan sandan Kano, CP Bakori.
Hoton kwamishinan yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori yana jawabi tare da jami'ansa kewaye da shi Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana kama mutanen ga manema labarai a hedkwatarsu da ke Kano a ranar Litinin, in ji Channels tv.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun yi ta'asa, sun hallaka jami'in 'dan sanda har lahira

'Yan sanda sun kama 'yan daba a zaben Kano

Ya ce an kama yan daban ne sakamakon shirin tsaro na musamman da aka aiwatar domin bayar da cikakken tsaro da kariya ga zaben.

“A yayin zaɓen, wanda aka gudanar a cikin mawuyacin hali, wasu marasa kishin ƙasa sun yi ƙoƙarin tada fitina ta hanyar shigo da ’yan daba da dama daga cikin Knao da wajen ta,” in ji Bakori.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kwato makamai da kayan zaɓe daga hannun mutanen da aka kama.

Abubuwan da aka kwato a hannun bata garin

Daga cikin abubuwan da ya ce sun kwato akwai bindiga guda daya, bindigu kirar gida guda biyar, sanduna guda 94, takubba guda 16, da adduna guda 18.

Sauran sun hada da makamai na gargajiya guda 32, wukake guda 18, baka guda ɗaya da kibau 23, da duwatsu da motoci 14 da ake zargin an yi amfani da su wajen tada rikici.

Kara karanta wannan

Kano: Yan sanda sun burma matsala bayan taimakon ɗan siyasa yana rabon kuɗi

Haka kuma ya ce yan sanda sun kwato akwatin kada ƙuri’u guda biyu, takardun ƙuri’u guda 163 da aka dangwale su, da kuɗi ₦4,048,000.00.

'Yan sanda sun gurfanar da wadanda aka kama

“Duka waɗanda aka kama an gurfanar da su a gaban Kotunan Majistare da ke Nomansland da Gyadi-Gyadi, Kano, domin fuskantar tuhuma bisa laifuffuka daban-daban na zaɓe,” in ji CP Bakori.
Kwamiahinan yan sandan Kano.
Hoton CP Ibrahim Adamu Bakori a hedkwatar yan sandan Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Ya lissafo tuhumar da ake musu da su haɗa da haɗa kai wajen aikata laifi, mallakar makamai masu haɗari, tsoratarwa, yawo ba tare da dalili ba bayan kaɗa ƙuri’a, kwace ko lalata kayan zaɓe, da kuma neman hana zaɓe.

Bakori ya yaba da aikin da jami’an tsaro suka yi tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi a ƙarƙashin kwamitin tsaro na zaɓe (ICCES), kamar yadda Leadership ta kawo.

An hukunta 'yan sanda a jihar Kano

A wani labarin, kun ji cewa an hukunta yan sandan da aka gani a faifan bidiyo su ma taimakawa dan siyasa wajen rabon kudi a jihar Kano.

Rundunar yan sandan ta tabbatar da cewa an ɗauki matakin ladabtarwa a kan jami’an daidai da abin da suka aikata.

Babban abin da ya fi daukar hankali game da bidiyon shi ne mutane sun yi zargin lamarin ya faru ne a lokacin zaben cike gurbi a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262