Otedola: Yadda Attajiri a Najeriya Ya Gagara Yin Makaranta, Ya Fadi yadda Ya Maimaita Aji

Otedola: Yadda Attajiri a Najeriya Ya Gagara Yin Makaranta, Ya Fadi yadda Ya Maimaita Aji

  • Fitaccen dan kasuwa, Femi Otedola ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta tun daga makarantar firamare zuwa sakandare
  • Attajirin ya ce ya sha wahala a makaranta ba tare da kyakkyawan sakamako ba wanda ya yi sanadiyyar rashin zuwansa jami'a
  • Otedola ya ce yana da sha’awar harkar kasuwanci fiye da karatu, inda ya fara aiki tare da mahaifinsa, abin da ya ja hankalinsa sosai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Daya cikin attajirai a Najeriya, Femi Otedola ya yi bayani kan wahalar da ya sha a makaranta saboda rashin kokari.

Otedola ya bayyana cewa kamar yadda ake tsammani bai gama jami'a ba saboda bai da sha'awar karatu domin ya fi son kasuwanci.

Yadda Otedola ya maimaita aji a makaranta
Attajiri Femi Otedola ya rubuta tarihin rayuwarsa. Hoto: Femi Otedola.
Source: Getty Images

Wahalar da Otedola ya sha kafin zama attajiri

Attajirin mai shekara 62, ya fada a cikin wani littafin rayuwarsa cewa ya fara karatu a makarantar ma'aikatan jami'ar Lagos a 1968, amma kullum yana samun sakamako maras kyau, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Wuraren da suka halatta saurayi ya kalla a jikin macen da zai aura a Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce iyayensa sun yi ta kokari domin ganin ya yi karatu mai zurfi amma hankalinsa bai makaranta ko kadan.

Ya ce:

“Iyayena sun saka ni makarantar ma'aikata ta jami'ar Lagos a 1968, a shekara shida.
“Amma akwai wani abu tsakanina da karatu; ba mu daidaita ba, Na gama firamare a 1974 bayan na maimaita aji.
"Ko lokacin da aka bar ni in wuce, kullum ina kasa a sakamakon jarabawa, sha’awata ba ta cikin karatu.”

Bayan kammala firamare, Femi Otedola a wancan lokaci ya wuce makarantar Methodist, Lagos, rashin tabuka komai a karatu ya ci gaba da zama matsala a can.

A 1977, bayan ya bayyana cewa ba ya samun ci gaba, iyayensa suka tura shi makarantar Baptist High da ke Oyo, makarantar kwana da aka kafa a 1945.

Ya kara cewa:

“Tunanin iyayena shi ne cewa dukkan ’yan uwana suna makarantar kwana, suna yin kokari, sun yi zaton wannan zai taimaka, amma babu wani abu da ya canza.

Kara karanta wannan

Nata'ala: Jarumin Kannywood ya roki taimako bayan faɗin halin da yake ciki

"Na fara aji uku a Olivet, kuma lokacin da nake kusa kammalawa, mahaifina ya kafa kamfanin, na fara sha’awar aiki a ciki, Na iya zama makaranta har sai na gama jarabawa, daga nan na daina gaba ɗaya; ban koma na ci gaba ba.
“Abin da nake so shi ne shiga kasuwanci. Mahaifina ya kula da ni ya kuma kusanto ni gare shi."
Femo Otedola ya fadi abin da yake sha'awa tun yana karami
Attajiri Femi Otedola ya rubuta tarihin rayuwarsa da ya ba mutane mamaki. Hoto: Femi Otedola.
Source: Instagram

Yadda Otedola ya bar makaranta domin kasuwanci

Duk da kuka da koke-koken mahaifiyarsa, Otedola ya daina makaranta gaba ɗaya don ya yi aiki da cikakken lokaci a kasuwancin mahaifinsa.

Ya kara girma inda ya zama babban manaja a kamfanin 'Impact Press' a 1987 yana da shekara 25.

Bayyanarsa game da tarihin karatunsa na iya ba mutane mamaki saboda da dama suna ganin ya yi digiri.

Wani lokaci, a shafin Wikipedia an rubuta cewa ya yi karatu a University of Lagos, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Otedola ya fadi yadda Yar'Adua ya rusa su

Kun ji cewa dan kasuwa, Femi Otedola ya koka kan yadda gwamnatin marigayi Umaru Yar'Adua ta dakile shi da Aliko Dangote.

Odetola ya bayyana cewa sun shirya mallakar matatun mai a Kaduna da Port Harcourt amma shugaba Yar'Adua ya rusa tsarin.

Ya ce sun kulla yarjejeniya na siyan hannun jari a matatun biyu a mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kafin ya sauka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.