Amurka, Birtaniya Sun Yi Magana bayan Kama Manyan 'Yan Ta'addan Najeriya

Amurka, Birtaniya Sun Yi Magana bayan Kama Manyan 'Yan Ta'addan Najeriya

  • Amurka da Birtaniya sun yaba da nasarar cafke manyan shugabannin kungiyar Ansaru a Najeriya
  • An kama Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a) da Mahmud al-Nigeri (Malam Mamuda) a wani babban samame
  • Nuhu Ribadu ya ce shugabannin sun dade suna kitsa hare-hare da garkuwa da mutane don yada ta’addanci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun nuna gamsuwa da yadda Najeriya ta cafke manyan shugabannin kungiyar Ansaru, wadda aka dade tana da alaka da Al-Qaeda.

Nasarar ta faru ne a karkashin jagorancin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Shugaba Donald Trump da Bola Ahmed Tinubu na Najeriya
Shugaba Donald Trump da Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta yabawa Najeriya ne a wani sako da ofishin jakadancinta ya wallafa a X bayan kama 'yan ta'addan.

Shugabannin da aka kama sun hada da Mahmud Muhammad Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, da kuma Mahmud al-Nigeri, wanda ake kira Malam Mamuda.

Kara karanta wannan

Ansaru: Barnar da jagogorin yan ta'adda suka yi da ba ku sani ba kafin cafke su

Dukkaninsu na cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya, Amurka, Birtaniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Amurka da Birtaniya sun yaba wa Najeriya

Kama 'yan ta'addan ya samu yabo daga hukumomin kasashen waje, inda suka bayyana shi a matsayin ci gaba mai girma a yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a yankin.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ce:

“Mun yaba da Gwamnatin Najeriya da jami’an tsaro bisa nasarar cafke shugabannin Ansaru, Abu Bara’a da Malam Mamuda. Wannan babban ci gaba ne a yaki da ta’addanci.”

Shi ma jakadan Birtaniya a Najeriya, Richard Montgomery, ya ce wannan babbar nasara ce da za ta taimaka wajen murkushe ayyukan ta’addanci.

Tribune ta wallafa cewa ya kuma taya NSA Ribadu da jami’an tsaro murna bisa jajircewa wajen aikin da suka gudanar.

Bayanin Malam Nudu Ribadu

Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa samamen ya kasance mai cike da hadari, amma an gudanar da shi bisa bayanan sirri da tsare-tsaren kwararru tsakanin watan Mayu zuwa Yuli 2025.

Ya ce Abu Bara’a ne jagoran kungiyar Ansaru, mai tsara garkuwa da mutane da fashi da makami don samar da kudin ta’addanci.

Kara karanta wannan

Saura Turji: Jami'an tsaro sun cafke shugaban kungiyar 'yan ta'addan Ansaru

Ribadu da ke ba shugaban Najeriya kan harkokin tsaro.
Ribadu, Mai ba shugaban Najeriya kan harkokin tsaro. Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Twitter

Ribadu ya ce Mamuda kuwa shi ne mataimakinsa na kusa, wanda ya kafa 'Mahmudawa' a kusa da Kainji, a iyakar jihohin Neja da Kwara zuwa Jamhuriyar Benin.

Tarihin Mahmuda da ta'addancinsa

Ribadu ya bayyana cewa Mamuda ya samu horo a kasar Libya tsakanin 2013 zuwa 2015 karkashin wasu kungiyoyi a kasashen Masar, Tunisiya da Aljeriya.

Rahotanni sun nuna cewa ya kware wajen amfani da makamai da kuma hada abubuwan fashewa.

An bayyana cewa duka shugabannin biyu sun shafe shekaru suna shirya kai hare-hare da sace mutane a Najeriya, abin da ya haifar da asarar rayuka da dukiya.

'Yan ta'adda sun yi hadari a Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewa wasu 'yan ta'adda sun yi hadari a jihar Nasarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun yi hadari ne yayin da suke dauke da miliyoyin Naira da suka karba a matsayin kudin fansa.

Daya daga cikinsu da aka kama ya bayyana cewa hadari ya rutsa da su ne yayin da suke kan hanyar zuwa raba kudin da suka karba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng