Wuraren da Suka Halatta Saurayi Ya Kalla a Jikin Macen da zai Aura a Musulunci
- Malamin addini, Dr Jamilu Yusuf Zarewa ya bayyana cewa Musulunci ya halatta saurayi ya kalli macen da yake son aura
- Ya ce mafi rinjaye daga cikin malamai sun takaita kallon fuska da tafin hannu kawai a matsayin abin da ya halatta
- A cewarsa, wasu malamai sun yarda a kalli sassan jiki na zahiri, amma ba tare da yawaita kallon da zai iya haifar da fitina ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Tambayoyi kan abin da ya halatta saurayi ya kalla daga budurwar da yake son aura suna ci gaba da tasowa a tsakanin matasa Musulmai.
Wannan batu ya zama daya daga cikin abubuwan da ke jan hankali domin ya shafi tsarin aure da zamantakewa a cikin al’umma.

Kara karanta wannan
An taso gwamna Kirista a gaba kan karɓar bashin bankin Musulunci, ya yi ƙarin haske

Source: Facebook
Sheikh Dr Jamilu Yusuf Zarewa ya yi karin haske kan wannan batu a shafinsa na Facebook, inda ya yi bayani da hujjoji daga hadisan Annabi Muhammad (SAW).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin kallon macen da za a aura
A cewar shi, addini ya tanadi damar da saurayi zai kalli abin da zai tabbatar da sha’awa ga matar da yake son aura, amma ya takaita wannan damar da ka’idojin da za su kare al’umma daga barna.
Dr. Jamilu Zarewa ya ambaci hadisin Annabi (SAW) wanda ya ce:
“Idan ɗayanku yana neman aure, to idan ya samu damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan.”
Malamin ya bayyana cewa an rawaito wannan hadisin ne daga Imam Abu Dawud, mai lamba ta 2082.
Hadisin ya tabbatar da cewa kallon da ya dace ana yinsa ne domin dalilin aure, ba don sha’awa ko wasa ba, kuma wannan ne yasa malamai suka yi sabani kan sashen jiki da ya kamata a kalla.
Ra’ayoyin malamai kan inda za a kalla
Sheikh Zarewa ya ce malamai sun kasu kashi uku kan wajen da ya kamata a kalla:
1. Na farko, mafi rinjaye sun ce fuska da tafin hannu ne kawai za a kalla. Fuska tana nuna kyawun mace, yayin da tafin hannu yake nuna yanayin jikinta gaba ɗaya.
2. Na biyu, wasu sun ce za a iya kallo fiye da haka, kamar wuya ko siffofin jiki da suke bayyana a zahiri ba tare da shigar bariki ba.
3. Na uku kuma, wasu malaman suna da ra’ayin cewa za a kalle ta cikin kayan da take sawa a gida, inda ta tsaya tana kallon saurayi sannan ta juya baya domin ya ga yanayin jikinta.
Dr Zarewa ya ce wannan ra’ayi ya fi dacewa da burin aure, domin yana tabbatar da cikakken sanin matar da zai aura.
Gargadi game da yawaita kallon budurwa
Duk da haka, malamin ya ja kunnen matasa cewa bai kamata su yawaita kallon ba, yana cewa wajibi ne a tsaya gwargwadon bukata kawai.

Kara karanta wannan
Wata 1 da rasuwar Buhari, ma'aikatansa sun yi hawaye, sun fadi kyawawan halayensa
Ya ce wannan shi ya sa yawaita zuwa zance ko kiran waya da ba bisa bukata ba, na iya rikidewa zuwa haramun saboda yana iya tayar da sha’awa da haifar da barna.

Source: Facebook
Maganar Gumi kan zuwan Isra'ila Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce zuwan Isra'ila Najeriya barazana ce ga Musulmai.
Bayan zuwansu Abuja, malamin ya ce za a fara tsammanin kashe shugabanni Musulmai a Najeriya.
Sheikh Gumi ya yi magana ne bayan wakilan Isra'ila sun gana da karamar ministar harkokin wajen Najeriya da shugabannin Kiristoci.
Asali: Legit.ng
