Sulhu: Sheikh Asada Ya Bankaɗo Wani Sirrin Malamai, Ya Yi Bakaken Addu'o'i ga Turji, Aliero

Sulhu: Sheikh Asada Ya Bankaɗo Wani Sirrin Malamai, Ya Yi Bakaken Addu'o'i ga Turji, Aliero

  • Sheikh Murtala Bello Asada ya fito da sabon bidiyo inda ya soki masu fakewa da sulhu da ‘yan ta’adda
  • Malamin ya ce dan bindiga mai suna Dan Sadiya ya karɓi miliyan bibbiyu a matsayin kudin fansa ba sulhu ba
  • Sheikh Asada ya tabbatar da cewa bayan an biya kuɗin fansa, Dan Sadiya ya kai hari inda ya sace mutane 27

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada ya sake fitar da wani bidiyo inda yake tona asirin masu fakewa da maganar sulhu da yan ta'adda.

Malami Asada ya koka kan yadda aka yaudari malamai ko dai a rashin sani ko kuma saboda son abin duniya.

Sheikh Asada ya caccaki masu sukarsa kan sulhu da yan bindiga
Sheikh Asada na daga cikin wadanda suka matsawa Bello Turji. Hoto: Sheikh Murtala Bello Sokoto, HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Sheikh Asada ya sake sukar kwamitin sulhu

Sheikh Asada ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Litinin.

Kara karanta wannan

Wuraren da suka halatta saurayi ya kalla a jikin macen da zai aura a Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon, malamin ya ƙaryata cewa kwamitin sulhu ne suka yi nasarar kwato wasu mutane daga hannun yan ta'adda.

Ya ce:

"Wallahi ku yi suka amma Murtala Asada yana ba da dalilai, dan bindiga da ake kira Dan Sadiya kudin fansa ya karba ku ka ce an yi sulhu.
"Dan Sadiya miliyan bib-biyu ya karba bayan ya karbi kudi ku ka zo ku yada cewa kun amso mutane ta hanyar sulhu.
"Wannan karya kuka yi, kun yi yaudara kuma an sanar da ku, farko uzurin da na yi musu ba su sani ba."
Asada ya tona asirin wani malami kan sulhu da yan bindiga
Sheikh Asada na shan suka daga malamai kan adawa da sulhu. Hoto: Sheikh Murtala Bello Sokoto, Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe.
Source: Facebook

Hujjojin da Asada ke kawowa kan yan bindiga

Malamin ya bayyana cewa akwai hujjoji cewa yan uwan wadanda aka sako sun bi kwamitin sulhu suna rokonsu su ba su yan uwansu tun da sun biya kudin fansa.

Ya kara da cewa:

"Yan uwan yaran nan ranar Talata sun same su a ital din Gusau da suka sauka suka fada musu sun biya kudin fansa.

Kara karanta wannan

Nata'ala: Jarumin Kannywood ya roki taimako bayan faɗin halin da yake ciki

"Kuma suka bi su har gidan mai suna fadin a bamu yan uwanmu mun biya kudin fansa, wani malamin ya ce don Allah ka da ku bata mana aiki.
"Wannan Dan Sadiya da suke cewa sun yi sulhu da shi karya ne, wallahi ko garin Gusau bai ba su bari ba sai da ya kai hari a ranar Alhamis a garin Kanwa."

Har ila yau, ta tabbatar da kai hari wasu ƙauyuka a ranar da ake maganar an ceto wasu mutane daga yan bindiga.

Ya ce mutanen Kanwa suna jinsa bayan ya kai hari ya dauke mutum 27 suna hannunsa, ya koma wasu kauyuka ya harbe mutum shida.

Addu'o'in da Asada ya yi wa yan bindiga

Sheikh Asada ya yi ruwan addu'o'i kan yan ta'adda musamman Bello Turji da Ado Aliero da Dogo Gide da ke addaban al'umma.

Malamin ya roki Allah ya tona asirin mutanen da ke son kawowa Turji mafia bayan kisan al'umma da ya yi.

Ya roki Allah ya tozarta masu neman yiwa Ado Aliero mafita mutumin da ya ce bai san adadin mutane da ya kashe ba.

Kara karanta wannan

Assadus Sunnah ya ƙure masu sukarsa kan zama da Turji, ya yi rantsuwa da Allah

"Turuzzan birni da suka jawo mana wannan abin Allah ya isan ma al'umma, ya Allah muna rokon ka ga wasu suna son kawowa Bello Turji mafita Allah ka tona masa asiri."

- Cewar Murtala Bello Asada

Manoma sun yaba da sulhu a Katsina

Kun ji cewa a wasu yankuna a Katsina zaman lafiya ya fara dawowa bayan sulhun da al’umma suka yi da ’yan bindiga.

Manoma sun koma gonaki cikin kwanciyar hankali, inda wasu suka ce shekaru da dama basu yi noma ba.

Duk da wannan ci gaba, akwai yankuna da hare-hare ke ci gaba, inda aka yi garkuwa da mutane a Kankara, Sheme da Kakumi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.