Alhaki Ya Kama Su: 'Yan Bindiga Sun Yi Hadari bayan Karbo Makudan Kudin Fansa
- ’Yan sanda a Nasarawa sun ce wasu masu garkuwa da mutane sun tsere bayan hatsari inda suka bar N6.9m da manyan bindigogi
- Rahotanni sun nuna cewa wani jami’in VIO ne ya fara gano bindiga da kudi a cikin motar kafin a mika su ga ’yan sanda
- Bincike ya kai ga cafke wani daga cikin gungun masu garkuwan wanda ya amsa laifin da ake tuhumar su da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa - Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa ta kama makamai da miliyoyin Naira daga hannun ’yan bindiga da suka tsere bayan hatsari a Garaku, karamar hukumar Kokona.
Hatsarin ya faru ne a safiyar Litinin da misalin ƙarfe 9:00 na safe, a kusa da wajen da jami'an VIO ke tsayuwa, lokacin da mota kirar Opel Vectra ta yi hatsari.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa 'yan bindigar sun tsere, amma jami’in VIO ya gano kudi da bindiga a cikin motar, kafin daga baya a gano karin makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me aka gano a motar 'yan bindigan?
The Cable ta rahoto cewa mai magana da yawun ’yan sanda a jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce sun samu kiran gaggawa bayan hatsarin, inda jami’ai suka isa wurin.
Jami’in VIO ya mika bindigar G3 da ya samu a motar tare da wasu kudi kafin daga baya aka tura motar zuwa ofishin ’yan sanda.
Bincike a ofishin ya gano karin makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47, bindigar Type 06, bindigar G3, tarin harsasai da kudi har N6.9m.
An cafke wani daga cikin 'yan bindigan
DSP Nansel ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin ’yan sanda da sojoji ya taimaka wajen cafke wani mutum mai suna Mohammed Tahir, mazaunin Barkin Ladi a jihar Filato.

Kara karanta wannan
Al Makura: Ƴan bindiga sun bi dare, sun sace hadimin tsohon gwamna, an bazama daji
A lokacin tambayoyi, wanda aka kama ya amsa cewa yana daga cikin gungun masu garkuwa da mutane bakwai da suka yi garkuwa da wani lauya a Nyanya, Abuja, inda suka karɓi kudin fansa.
Ya kara da cewa shi da wani abokinsa suna kan hanyarsu ta zuwa Jos domin rabon kudin garkuwa kafin hatsarin ya rutsa da su.

Source: Facebook
Matakan da 'yan sanda suka dauka
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Shettima Jauro-Mohammed, ya ba da umarnin mika kayan da aka kwato tare da wanda aka kama ga sashen binciken manyan laifuffuka (SCID) a Lafia.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da neman sauran ’yan bindigan da suka tsere, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da kai rahoto ga jami’an tsaro.
DSP Nansel ya yi kira da cewa, hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro ne kadai zai taimaka wajen magance matsalar garkuwa da mutane da ta addabi al’umma.
Yaran Bello Turji sun kai hari Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin yaran dan ta'adda Bello Turji ne, sun kai hare-hare Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shafe kwana uku suna kai farmaki kan mutane a yakuna daban daban na jihar.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an kashe wani jami'in soji tare da sace matafiya da dama yayin hare haren.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
