Daga ƙarshe, An Ƙwamushe Ɗan Wanda Ya Kafa Boko Haram, Marigayi Mohammed Yusuf
- Hukumar tsaro ta Najeriya ta taimakawa kasar Chadi wurin tabbatar da kama wasu hatsabiban yan ta'adda
- Sojojin Chadi sun kama ɗan marigayi Mohammed Yusuf, wanda shi ne ya kafa kungiyar Boko Haram a Najeriya
- An kama matashin mai shekaru 18 tare da wasu biyar da ake zargi suna da alaƙa da ISWAP a wani samame
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Njamena, Chad - Hukumomi a kasar Chadi sun kama wani matashi ɗan marigayi Mohammed Yusuf, wanda ya kafa kungiyar Boko Haram.
Wannan nasara ta kama matashin mai shekaru 18 ta afku ne bayan samun bayanan sirri daga rundunar sojojin Najeriya.

Source: Facebook
An cafke dan marigayi Mohammed Yusuf a Chadi
Rahoton Zagazola Makama ya ce kasar Chadi ba ta san matashin da sanin asalinsa ba, sai da Najeriya ta sanar da ita.
An bayyana hakan ne ta hanyar bayanan sirri da jami’an tsaro na Najeriya suka bayar ta haɗin gwiwa na sojojin MNJTF.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kama matashin da ya fara gabatar da kansa da suna Abdurrahman Mohammed Abdallah tare da wasu mutum biyar da ake zargi.
Sauran sun haɗa da Hassan Abdurrahman wanda ake ganin mai kula da kayayyakin tsaro ne, Abubakar Mohammed mai ɗaukar mambobi, Abubakar Ali Madou wanda ake zargin ya ke kula da makamai.
Yadda aka kama 'yan ta'adda a Chadi
Wadannan mutane an cafke su ne yayin wani samame na yaƙi da ta’addanci a Chadi.
Daga baya jami’an tsaro suka tabbatar cewa matashin da aka kama shi ne Muslim Mohammed Yusuf, kanin Habib Yusuf wanda ake kira Abu Mus’ab Al-Barnawi, shugaban ISWAP.
Hakan ya nuna cewa yana jagorantar wata ƙungiya mai mutane shida a yankin Tafkin Chadi.
Hotunan da aka samu sun nuna matashi siriri mai sanye da riga ta wasanni launin shuɗi, wanda yake kama da mahaifinsa.

Source: Twitter
Rundunar tsaro a Chadi ta tabbatar da kamun amma ba ta bayyana cikakken bayanai ba har sai da Najeriya ta shiga.
Wata majiya ta ce:
“Wannan ba kame na yau da kullum ba ne, an haife shi a Najeriya kafin tarzomar 2009, kuma yanzu yana ƙoƙarin kafa kansa a ISWAP.” .
Mutuwar Mohammed Yusuf a hannun jami'an tsaro
Sojoji sun kama Mohammed Yusuf, wanda ya kafa Boko Haram, sannan daga baya aka kashe shi a hannun ’yan sanda a Maiduguri a 2009.
Wannan ne ya tayar da rikicin Boko Haram wanda ya bazu a Najeriya da makwabtan ƙasashe, cewar Daily Trust.
Bayan rasuwarsa, ɗansa babba Habib Yusuf ya zama shugaban ISWAP, yanzu kuma ana zargin Muslim Yusuf cewa shirya shi domin ya ci gaba da aikin ta’addanci.
Illar da kamun zai iya yiwa ISWAP
Masana sun bayyana cewa wannan kamun ya jefa ISWAP cikin matsala da jawo tasgaro ta fuskar dabaru da kuma tunani.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa
A cewar masana, kama ɗan Yusuf zai iya rage karfi wajen jawo sababbin mabiya, kuma ya nuna yadda ake ci gaba da gadon ra’ayin ta’addanci cikin iyalai.
Borno: Boko Haram sun sace Fasto
Kun ji cewa yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun yi ta'asa a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.
Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wani limamin cocin Katolika.
Tsagerun ba su tsaya iya nan ba, sai da suka yi awon gaba da wasu matafiya bayan sun tare motocinsu a kan hanya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

