An mayar da 'yan sandan da ake zargi da kisan shugaban kungiyar Boko Haram bakin aiki

An mayar da 'yan sandan da ake zargi da kisan shugaban kungiyar Boko Haram bakin aiki

- Jami'an 'yan sandan Najeriya biyar da ake zargi da kashe shugaban kungiyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf sun koma bakin aiki

- An dakatar da jami'an 'yan sandan ne daga aiki bisa zarginsu da kashe Muhammad Yusuf bayan jami'an soji sun damka shi a hannun su

- Tun shekarar 2015 kotu ta wanke 'yan sandan bisa zargin da ake yi masu na kisan Muhammad Yusuf

Hukumar kula da aikin 'yan sanda (PSC) ta mayar da jami'an 'yan sanda biyar da ake zargi da kashe shugaban kungiyar, Muhammad Yusuf, bakin aikinsu.

An dakatar da jami'an ne bisa tuhumar su da kashe Muhammad Yusuf bayan jami'an soji sun damka shi a hannun hukumar 'yan sanda a shekarar 2009.

An mayar da 'yan sandan da ake zargi da kisan shugaban kungiyar Boko Haram bakin aiki
Muhammad Yusuf

Tun a watan Disamba na shekarar 2015 wata kotun Abuja ta wanke jami'an 'yan sandan daga aikata laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Kakakin hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya tabbatar da mayar da jami'an bakin aiki.

"Da gaske ne mun mayar da su bakin aiki bayan wani sako na musamman da shugaban 'yan sanda ya aiko mana," Ani ya shaidawa kamfanin labarai na AFP.

DUBA WANNAN: Kungiyar matasan arewa ta roki Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

Wani mai nazarin harkokin tsaro, Amaechi Nwakolo, ya bayyana mayar da jami'an 'yan sandan da cewar abin damuwa ne. A cewar sa, mayakan kungiyar Boko Haram na ci gaba da tayar da kayar baya ne saboda har yanzu ba a hukunta kowa ba dangane da kisan shugaban su.

Rikicin Boko Haram da ya fara tun shekarar 2009, ya yi sanadin asarar rayuka a kalla 20,000 tare da raba kimanin mutane miliyan 2.6 da muhallinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng