NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama Mai Yawa a Kaduna, Neja da Jihohin Arewa 13 Ranar Talata
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama a Zamfara, Kaduna, Kebbi da wasu jihohin Arewa a ranar Talata
- A Arewa ta Tsakiya, NiMet ta ce za a samu ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Niger, Plateau, da wasu jihohin daga safiya zuwa dare
- A Kudancin Najeriya, ba za a samu ruwan sama da safe ba amma ana iya samun yayyafi da yamma a Ogun, Oyo da wasu jihohi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A daren ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025, hukumar da ke hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Talata.
Hasashen da NiMet ta ce zai yi aiki daga karfe 12:00 na safiyar Talata, 19 ga Agusta, 2025 zuwa karfe 11:59 na daren ranar, ya nuna cewa za a samu ruwan sama a wasu sassan kasar nan.

Kara karanta wannan
'Ka auri ƴar zamani,' An ba Adam A Zango shawarar yadda zai riƙe sabuwar amaryarsa

Source: Original
Hasashen yanayi a wasu jihohin Arewa
A hasashen da hukumar ta wallafa a shafinta na X, NiMet ta ce za a samu ruwan sama a jihohin Zamfara, Kaduna, and Kebbi a safiyar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kuma sa ran samun ruwan sama a wasu sassan jihohin Zamfara, Jigawa, Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Bauchi, da Gombe a yammacin ranar.
A Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sa ran ruwan sama zai sauka a Abuja da jihohin Nasarawa da Niger a safiyar Talata.
Da yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran ruwan sama zai sauka a Abuja da wasu sassan jihohin Nasarawa, Niger, Plateau, Benue, Kwara, da Kogi.
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
A Kudancin Najeriya kuwa, hukumar NiMet ta ce hasashenta ya nuna cewa ba za a samu ruwan sama a safiyar ranar Talata a jihohin shiyyar ba.
Amma, NiMet ta ce za a iya samun yayyafi a wasu sassan jihohin Ogun, Oyo, Rivers, Ebonyi, Delta, Lagos, Cross River, da Akwa Ibom a yammacin ranar.
Wannan hasashen ya nuna cewa babu wata jiha a Najeriya da ake fargabar za ta fuskanci ambaliyar ruwa a ranar Talata.
Shawarwarin NiMet ga 'yan Najeriya
NiMet ta shawarci jama'a da su ci gaba da yin taka tsantsan game da yiwuwar ambaliyar ruwa, iska mai ƙarfi, da kuma katsewar al'amuran yau da kullun.

Source: Original
An kuma shawarci direbobi su guji tuki yayin ruwan sama mai yawa don kaucewa haɗurra sannan kada a fake a karkashin bishiyoyi yayin guguwa don gujewa fadowar reshe.
Hukumar ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayi na filin jirgin kafin tsara zirga-zirgarsu.
NiMet ta bukaci jama’a su ci gaba da samun sababbin bayanai daga shafinta: www.nimet.gov.ng domin tsare lafiya, rayuka da kuma dukiyoyinsu.
Karanta hasashen a nan kasa:
Ambaliyar ruwan kwanaki 3 a wasu jihohi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta fitar da hasashen ruwan sama da tsawa na tsawon kwanaki uku a wasu jihohin Najeriya.
NiMet ta ce jihohin Arewacin Najeriya bakwai da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa daga ranar Lahadi, 17 ga Agusta zuwa Talata, 19 ga Agusta, 2025.
NiMet ta shawarci jama’a da su guji tukin mota a lokacin ruwan sama mai yawa yayin da ta bukaci jihohin da ke cikin hadarin ambaliya su yi shirin gaggawa.
Asali: Legit.ng
