An Taso Gwamna Kirista a Gaba kan Karɓar Bashin Bankin Musulunci, Ya Yi Ƙarin Haske

An Taso Gwamna Kirista a Gaba kan Karɓar Bashin Bankin Musulunci, Ya Yi Ƙarin Haske

  • Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi karin haske bayan taso shi a gaba kan karbar bashin bankin Musulunci
  • Gwamna Otti ya bayyana cewa bashin dala miliyan 125 daga Bankin Raya Musulunci, an amince da shi ne domin ci gaban ayyuka
  • Ya ce za a yi amfani da bashin wajen gine-gine da hanyoyi a Abia, tare da samar da ayyukan yi sama da 3,000

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia - An taso Gwamna Alex Otti na jihar Abia kan alaka da bankin raya Musulunci a matsayinsa na Kirista.

Gwamna Otti ya fayyace cewa bashin dala miliyan 125 da gwamnatin tarayya ta amince da shi na Bankin Raya Musulunci, ba shi da wata alaka da addini.

Gwamna Kirista ya yi karin haske kan karbar bashin bankin Musulunci
Gwamna Alex Otti na jihar Abia yayin taron majalisar zartarwa a Umuahia. Hoto: Alex C. Otti.
Source: Facebook

Gwamna ya fayyace dalilin alaka da bankin Musulunci

Kara karanta wannan

Wuraren da suka halatta saurayi ya kalla a jikin macen da zai aura a Musulunci

Yayin hira da ’yan jarida a Umuahia, Otti ya ce bashin zai taimaka wajen gudanar da ayyukan raya kasa, tare da tabbatar da gaskiya da adalci, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce manufarsa kawai ita ce ci gaban ayyukan raya kasa, sabanin yadda wasu ke tunani ko yada jita-jita a tsakaninsu.

Ya ce:

“Yanzu kuna damuwa da dala miliyan 125? Kuna damuwa cewa daga bankin raya Musulunci yake? Babu dalilin damuwa.”
Ya kara da cewa kudi ba su da launi, don haka abin da ya fi muhimmanci shi ne a yi amfani da su wajen ci gaban al’umma.
“Kudi ba shi da launi. Ko daga shaidan ne ko daga sama. Muhimmanci shi ne a yi amfani da shi yadda ya dace.”

- Cewar Gwamna Otti

Gwamna Otti ya godewa Tinubu kan taimaka masa
Bola Tinubu da Gwamna Alex Otti a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Wasu irin sharuda bankin Musulunci ya gindaya?

Gwamna Otti ya ce Kwamishinan Kudi zai bayyana karin bayani cikin kwanaki masu zuwa inda ya ce sharuɗɗan bashin suna da sauƙi bayan ya nazarce su.

Ya tunatar da cewa tun a zaman majalisar zartarwa an amince da bashin, wanda zai rufe aikin gina hanyoyi sama da kilomita 126 a Aba da 35 a Umuahia.

Kara karanta wannan

Nata'ala: Jarumin Kannywood ya roki taimako bayan faɗin halin da yake ciki

Haka kuma, ya ce wannan aiki mai girma dala miliyan 263.80 ne, inda IsDB ta bayar da dala miliyan 125, Bankin Raya Afirka ya bayar da dala miliyan 100.

Gwamnan ya yabawa Tinubu, Majalisa da ministoci

Za a gudanar da aikin ne ta ma’aikatar ayyuka ta jihar Abia, karkashin kulawar kwamitin jagoranci na musamman da aka kafa.

Otti ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da wannan bashi da kuma jagoranci mai kyau, Tribune ta ruwaito.

Ya kuma yaba wa majalisar dokoki da ministoci da sauran shugabanni bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da an kammala tsarin.

Gwamna Otti zai dauki malamai 4,000 aiki

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Alex Otti na Abia ya ce za a dauki sababbin malamai 4,000 domin cike gibin da ake da shi a makarantu.

Otti ya ce hakan na da nasaba da yawan ɗalibai da aka samu tun bayan kaddamar da tsarin ilimi kyauta da gwamnati ta ayyana.

Gwamnan ya ce baya ga gyaran makarantu da ɗaukar malamai, gwamnati na shirin kammala gyaran asibitocin matakin farko guda 200.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.