Ribadu: Hadimin Tinubu Ya Tsame Mutum 1 a Gwamnati, Ya Faɗi Amfaninsa a Wata 25

Ribadu: Hadimin Tinubu Ya Tsame Mutum 1 a Gwamnati, Ya Faɗi Amfaninsa a Wata 25

  • Hadimi a Fadar shugaban kasa ya yi magana kan abubuwan da mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ke yi
  • Hadimin ta yabawa Ribadu bayan wata 25 da ya yi yana jagorantar yaki da ta’addanci, 'yan ta’adda da sauran barazanar tsaro
  • Dada Olusegun ya ce an samu zaman lafiya a wurare masu rikici, an raunana IPOB, kuma an inganta tsaro da jin dadin sojoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Hadimi a Fadar shugaban kasa ta yi magana musamman kan mai ba Bola Tinubu shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Hadimin Fadar shugaban ta yaba da aikin Nuhu Ribadu, tana kiran wata 25 da ya shafe a ofis a matsayin abin alfahari ga Najeriya.

Hadimin Tinubu ya yabawa kokarin Ribadu a gwamnatinsa
Malam Nuhu Ribadu na daga cikin wadanda ake yabo a gwamnatin Tinubu. Hoto: Nuhu Ribadu, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yabo da Ribadu ya samu a gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

Ansaru: Barnar da jagogorin yan ta'adda suka yi da ba ku sani ba kafin cafke su

Hakan na cikin wani rubutu da hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa na X a jiya Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun ya ce Ribadu ya yi yaki da ta’addanci, 'yan fashi da sauran barazanar tsaro ta kowane bangare a Najeriya baki daya.

Ya bayyana cewa nadin Ribadu ya sake fasalin ofishin NSA tare da kawo gagarumin sakamako a yankuna daban-daban.

Ribadu ya zama mashawari bayan shugaban kasa ya canza manyan hafsoshin tsaro tare da sake tsarin tsaron kasa.

Hadimin Tinubu ya yabawa Ribadu kan kokarin da yake yi
Shugaba Bola Tinubu yayin wani taro a birnin Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Kokarin Nuhu Ribadu a bangaren tsaro

Olusegun ya ce Nuhu Ribadu ya fifita haɗin gwiwar hukumomin tsaro da bayanan sirri, ya karfafa hadin kai tsakanin hukumomi tare da amfani da dangantakarsa ta kasa da kasa don kara ingancin leken asiri.

Ya bayyana wasu daga cikin nasarorin Ribadu: Kama masu shirya hare-haren ta’addanci kamar na jirgin kasa Abuja-Kaduna a 2022.

Ya ce:

“Haka nan, raguwar hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane: dakarun soji sun fatattaki shugabannin 'yan bindiga a Zamfara, Katsina, Kaduna da Sokoto, sun kubutar da dubban mutane, suka dawo da tsaro hanyoyi.

Kara karanta wannan

Saura Turji: Jami'an tsaro sun cafke shugaban kungiyar 'yan ta'addan Ansaru

“Karuwar samar da man fetur: Fitar da danyen mai ta tashi daga kasa da miliyan daya a rana a 2023 zuwa kimanin 1.8m, bayan dakile satar mai da lalata bututun.
“Zaman lafiya a wuraren rikice-rikice: Fadan kabilanci a Kudancin Kaduna, Filato, Taraba da Benuwai sun ragu, da hadin kai tsakanin jami’an tsaro da sulhu.
“Raguwar karfin IPOB/ESN: Hare-haren sojoji da matakan doka kan hanyoyin samun kudaden waje na IPOB sun raunana kungiyar, yayin da dokar zaman gida ta ragu.”

Hadimin Tinubu ya ce ribadu ya samu goyon bayan Tinubu ta hanyar sabbin kayan aikin soja, inganta walwalar sojoji, da kara amfani da fasahar leken asiri.

Olusegun ya ce duk da cewa har yanzu akwai matsaloli, tsarin tsaro ya fi karfi, hanyoyi sun fi aminci, samar da mai ya daidaita, kuma manoma suna komawa gonaki.

Ribadu ya faɗi barnar Ansaru a Najeriya

Mun ba ku labarin cewa mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi karin haske kan jagororin yan ta'adda da aka cafke.

Ribadu ya bayyana cewa an kama manyan shugabannin kungiyar Ansaru da suka jagoranci harin gidan yarin Kuje.

Daga cikin wadanda aka cafke akwai Mahmud Usman, wanda ake kira Abu Bara’a, da mataimakinsa Malam Mamuda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.