FIRS, Kwastam da Hukumomi 3 Sun Tatso Naira Tiriliyan 21 daga Hannun Ƴan Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta samu N21.22tn daga hukumomi biyar a watanni shida na 2025, duk da haka har yanzu tana neman rancen kudi
- Hukumar FIRS ta fi kowa tara haraji da N13.76tn, sai NUPRC da ta samu N5.21tn, sannan Kwastam ta tara N2.02tn daga kuɗin shigo da kaya
- Jimillar kuɗaɗen da aka tara ya kai kashi 58% na hasashen kasafin kuɗi na 2025, alamu na cewa gwamnati za ta iya zarce burinta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta samu kusan Naira tiriliyan 21.22 daga harajin da manyan hukumomi biyar suka tattara a cikin watanni shida na farkon 2025.
Wannan ya nuna cewa gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga ta hanyar ƙarfafa hanyoyin tatsar 'yan kasa, tsaurara dokoki, tare da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗe – na haraji da wanda ba haraji ba.

Kara karanta wannan
'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi

Source: Twitter
Tatso haraji don aiwatar da kasafin 2025
Sai dai kuma, duk da samun N21.22tn a cikin watanni shida kacal, hakan bai hana gwamnatin neman rance da tallafi daga ƙasashen waje ba, in ji jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan hukumomin gwamnati biyar sun samu kudaden shiga daga Janairu zuwa Yuni, 2025 ta hanyar kudaden haraji, kudin kwastam da kuɗin mai, wanda ya zarce tsammanin da aka yi.
Bayanan da aka tattara a cikin rahotannin kuɗi da aka gabatar wa Hukumar Raba Kuɗin Tarayya (FAAC) a ranar Litinin, sun nuna yadda gwamnati ta ƙara kaimi wajen tara kudaden shiga karkashin kasafin kuɗin 2025.
Idan ba a manta ba, a bara, bayan amincewar majalisar dattawa, gwamnatin tarayya ta amince da kasafin kuɗi na N54.2tn da aka raɗa masa suna “Kasafin daidaita lamura: Tabbatar da zaman lafiya, gina arziki”.
An tsara za a samar da N36.35tn na kasafin 2025 daga faɗaɗa haraji, ƙarfafa ayyukan kwastam, samun ƙarin riba daga kamfanonin gwamnati da kuma karɓar kuɗin mai.
N21.22trn: Harajin da hukumomi 5 suka tara
Bayan shafe watanni shida da fara aiwatar da kasafin kuɗin 2025, sababbin bayanai sun nuna cewa hukumomi biyar sun tara sama da N21.22tn, wanda ya zama rabin burin gwamnati na shekara ɗaya.
Rahoto ya nuna cewa Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta fi tatsar haraji daga hannun 'yan Najeriya, inda ta tara N13.76tn tsakanin Janairu zuwa Yuni, 2025.
Sai Hukumar Kula da Ayyukan Man Fetur ta NUPRC da ta tara N5.21tn daga kudaden mai da dangoginsu, yayin da Kwastam (NCS) ta bayar da N2.02tn daga kudaden shiga na harajin kaya da sauran kuɗaɗe.
Ma’aikatar Ma’adinai da Karafa ta tara N32.39bn, yayin da kamfanin NNPCL ya ruwaito samun N197.8bn daga ayyukan kasuwancinsa, cewar rahoton Economic Confidential.

Source: Twitter
Gwamnati ta cimma 58% na kudin shiga
Sai dai a cikin rahotonta na kowane wata, NNPCL ya bayyana cewa ya riga ya tura N6.96tn a matsayin biyan kudin doka tsakanin Janairu da Yuni, 2025, abin da bai yi daidai da bayanan da aka gabatar wa FAAC ba.
Jimillar kuɗaɗen da aka tara sun kai kusan kashi 42.23% na burin kuɗin shiga na N50.2tn da aka sa wa FIRS (N25.2tn), NUPRC (N15tn) da NCS (N10tn).
Haka kuma ya kai kashi 58% na hasashen kuɗaɗen gwamnati na N36.35tn a 2025, abin da ke nuna cewa idan aka ci gaba da wannan ƙoƙari, gwamnati za ta iya zarce burinta na shekarar.
Tinubu ya sanya hannu kan dokar gyaran haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin gyaran haraji huɗu, yana mai cewa "sabon babi ne ga Najeriya".
Waɗannan sababbin dokokin za su daidaita haraji, haɓaka hanyoyin kuɗaɗen shiga, da kuma inganta yanayin kasuwanci a Najeriya baki ɗaya.
Dokokin sun haɗa da dokar haraji, dokar gudanar da haraji, dokar kafa hukumar haraji da kuma dokar kafa hukumar haɗin gwiwar haraji ta kasa.
Asali: Legit.ng

