Gwamnatin Tinubu za Ta Fara ba Iyaye Tallafin Kudi domin Tura 'Ya'yansu Makaranta
- Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin BETA domin dawo da yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma inganta harkar karatu a Najeriya
- Shirin ya haɗa da biyan kuɗi ga iyaye mata don ƙarfafa halartar yara a makarantu tare da bayar da tallafin ciyarwa da kayan karatu
- An ware kuɗi da dama don koyar da matasa sana’o’i, gyaran makarantu, da kuma tallafin ilimi a fannoni daban-daban a fadin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon shirin gyaran ilimi da ta kira BETA domin magance matsalar yara da ba sa zuwa makaranta da kuma tabbatar da ingancin tsarin koyarwa.
Ministan ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya bayyana shirin a Abuja, inda ya ce shirin zai bai wa iyaye mata tallafin kuɗi domin su tura ’ya’yansu makaranta tare da kula da halartar su a kai a kai.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa ya ce wannan tsari ya haɗa da shirin mayar da yara makaranta tare da hadin gwiwa da hukumar almajirai ta kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanin da ministan ya yi ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin rajista da sauran kuɗin shiga makarantar yaran.
Manufar shirin BETA a Najeriya
Ministan ya bayyana cewa shirin BETA zai magance matsalolin da suka shafi ilimi a ƙasar nan ciki har da ƙarancin malamai, tsofaffin manhajoji, da rashin isassun kayan aiki.
A cewarsa, gwamnati za ta sake horar da malamai tare da horar da matasa miliyan biyar cikin shekaru huɗu masu zuwa domin karfafa fannin koyar da sana’o’i da fasaha.
Za a ba dalibai tallafin karatu a Najeriya
A halin yanzu, malamai 270 na fasaha sun samu horo na zamani a Ibadan, yayin da sama da malamai 6,000 na makarantu masu zurfi suke samun horo kan basirar fasahar zamani.
Ya ce daga zangon karatu na 2025/2026, ɗaliban makarantun fasaha a jihohi da tarayya za su samu ilimi kyauta, ciyarwa, ɗakin kwana, da kuma tallafin kuɗi na N22,500 a kowane wata.

Asali: Twitter
Gyaran makarantu da sabon tsarin STEMM
Alausa ya bayyana cewa sama da Naira biliyan 80 aka ware domin gyaran makarantun gama-gari da kuma sabunta makarantu 38 na fasaha a fadin ƙasa.
The Nation ta rahoto ya ce an ƙaddamar da shirin STEMM wanda ya shafi ilimin kimiyya, fasaha, lissafi da kuma ilimin lafiya, tare da samar da tallafi har zuwa Naira miliyan 50.
Tallafin karatu da sababbin manhajoji
Ministan ya sanar da ƙarin kuɗin tallafin karatu da za a bai wa ɗalibai a kowane mataki, inda ɗaliban digiri za su samu N450,000, masu digiri na biyu N600,000.
Ya bayyana cewa dalibai masu digiri na uku za su samu tallafin karatu na N750,000 a duk shekara.
Bugu da ƙari, an sabunta manhajar makarantu domin ta dace da ƙalubalen ƙarni na 21, ta hanyar ƙara darussa kan tunani mai zurfi, ilimin fasaha, kasuwanci, da ɗabi’a.
Za a hukunta masu satar amsa a Najeriya

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta bude sabon shiri, za a hada matasa da masu daukar aiki a duniya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta kafa kotun hukunta dalibai masu satar amsa.
Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana haka a wani taro da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa shirin zai shafi dalibai a matakai daban daban, musamman masu rubuta jarrabawar kammala sakandare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng