Daga Lahadi: Ruwan Sama na Kwana 3 Zai Jawo Ambaliya a Gombe da Jihohin Arewa 7
Abuja - Hukumar da ke hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen ruwan sama da tsawa na tsawon kwanaki uku a wasu jihohin Najeriya.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legit Hausa ta zakulo jihohin Arewacin Najeriya bakwai da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa daga ranar Lahadi, 17 ga Agusta zuwa Talata, 19 ga Agusta, 2025.

Source: Original
Hasashen yanayi na ranar Lahadi
Jaridar Punch ta rahoto NiMet ta bayyana cewa za a samu ruwan sama a Jigawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, Yobe, Borno da Adamawa da safiyar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, hukumar ta yi hasashen hadari tare da ruwan sama a wasu sassan Zamfara, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Bauchi, Gombe, Sokoto, Kebbi, Yobe, Borno, Adamawa da Taraba da yammacin ranar.
Hukumar ta yi gargadin yiwuwar ambaliya a Kebbi, Gombe da Bauchi a lokacin hasashen.
A Arewa ta tsakiya kuwa, hukumar NiMet ta ce ana sa ran ruwan sama kadan a Plateau, Abuja da Neja da safiyar Lahadi
A yammaci zuwa dare kuma, za a samu ruwan sama kadan a Abuja, Nasarawa, Neja, Plateau, Benue, Kwara da Kogi.
Hukumar ta kara da cewa akwai yiwuwar ambaliya a Neja, Plateau, Kogi da Benue.
Hasashen yanayi na ranar Litinin
A ranar Litinin, NiMet ta yi hasashen hadari da ruwan sama a Bauchi, Borno, Adamawa, Gombe, Taraba, Yola, Kano, Katsina, Yobe, Jigawa, Sokoto, Zamfara, Kebbi da Kaduna.
A Arewa ta tsakiyar kasar, ana sa ran ruwan sama kadan a Abuja, Nasarawa, Benue da Neja da safe.
Da yamma zuwa dare kuma, ana hasashen ruwan sama kadan a wasu sassan Neja, Plateau, Kwara da Benue.
Hasashen yanayi na ranar Talata
A Talata, NiMet ta yi hasashen ruwan sama a Katsina, Sokoto, Zamfara, Yobe, Adamawa, Borno, Jigawa, Kano da Kaduna da safe.
Da yamma zuwa dare, ana hasashen hadari da tsawa hade da ruwan sama a Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Jigawa, Kano, Kaduna da Adamawa.
A yankin tsakiyar kasar, NiMet ta ce ana hasashen hadari da safe, yayin da yamma zuwa dare za a samu ruwan sama a Abuja, Neja da Plateau, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Original
Gargadi da shawarwari daga NiMet
NiMet ta shawarci jama’a da su guji tukin mota a lokacin ruwan sama mai yawa. Ta bukaci jihohin da ke cikin hadarin ambaliya su yi shirin gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi.
An shawarci manoma su guji zuba takin zamani ko maganin kwari kafin ruwan sama don kauce wa salwantar abinci.
"A samar da tufafi masu dumi ga masu rauni saboda sanyi da dare, sannan a daure kayayyaki masu saukin motsi don kauce wa faduwa yayin iska.
"A cire na’urorin lantarki daga soket da kuma guje wa tsayawa kusa da manyan bishiyoyi don kauce wa hadarin faduwar rassa."
- NiMet.
Haka kuma, hukumar ta shawarci kamfanonin jiragen sama su nemi bayanin yanayi daga NiMet don tsara zirga-zirgarsu yadda ya dace.
Ma'aikatan NiMet sun shiga yajin aiki
A wani labarin a can baya, mun ruwaito cewa, ma’aikatan NiMet sun fara yajin aiki, inda suka rika zagaye filayen jiragen sama don tabbatar bin umarnin.
Ma’aikata hukumar hasashen yanayin sun koka da karancin albashi, suka ce wasu suna karɓar rance don biyan kuɗin haya da kudin makarantun 'ya'yansu.
Yayin da jagoran masu yajin aikin, Paul Ogohi ya ce ma'aikatan NiMet na mutuwa kamar kaji, ya ce 70% na fama da hawan jini, 90% na da matsalolin ido.
Asali: Legit.ng


