Zaɓen Cike Gurbi: Yadda 'Yan Sandan Kano Su ka Kama 'Yan Daba sama da 100

Zaɓen Cike Gurbi: Yadda 'Yan Sandan Kano Su ka Kama 'Yan Daba sama da 100

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta tabbatar da kama sama da mutum 100 da ake zargin ’yan daba ne a Bagwai yayin zaben cike-gurbi
  • Kwamishinan hukumar INEC na Kano, Abdu Zango, ya ce duk da samun rahotannin 'yan daba na yawonsu da mugayen makamai, ana zabe lafiya
  • Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da kama wadanda ake zargin sun isa filini zabe ne domin su rikirkita al'amura, kuma za a hukunta su nan gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta tabbatar da kama sama da mutum 100 da ake zargin ’yan daba ne a Bagwai yayin zaben cike-gurbi.

Kwamishinan INEC na Kano, Abdu Zango, ne ya tabbatar da kamen, inda ya ce an yi kyakkyawan shirin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

APC ta tsorata, ta bukaci INEC ta soke duka zaben cike gurbi a Kano

Rundunar 'yan sandan Kano ta yi kame
H-D: Wasu daga cikin ƴan daban da aka kama, jami'an ƴan sandan Kano Hoto: Aminu Abba Sharif/Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wadanda ake zargi da shirin aikata laifin, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta tabbatar da kama ’yan daba 100 a Kano

A ganawarsa da manema labarai, Kwamishinan INEC na jihar Kano, Abdu Zango, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun zage damtse domin tabbatar da cewa an kammala zabe lafiya.

Ya ce:

“Dukkannin waɗanda muka gani an tattara su, kuma tsarin zabe na ci gaba da gudana lafiya. Na yi matuƙar farin ciki. An kawo kayan zaɓe masu muhimmanci a kan lokaci, kuma aka fara kada ƙuri’a da misalin 8:30 na safe a mafi yawan wurare.

Zango ya ƙara da cewa, ko da yake an samu jinkiri a wasu wurare saboda lalacewar motoci da kuma yunkurin wasu kungiyoyi na tada hankali, jami’an tsaro sun yi tsayin daka.

Kano: An kama 'yan daba a Shanono

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Jami'an tsaro sun cafke shugaban PDP da jami'an INEC

Daya daga cikin wadanda ke sa ido a kan yadda zaben ke gudana a karamar hukumar Shanono, Kamal Umar Kurna ya ce sun ga yadda jami'an tsaro su ka kama wasu makamai.

Jami'an yan sandan Kano
Kwamishinan yan sandan Kano, Ibrahim Bakori da tawagarsa Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

"Muna cikin asibitin karamar hukumar Shanono, asibitin sha ka tafi. Kwamishinan 'yan sandan Kano tare da hadin gwiwar rundunonin tsaro sun ziyarci asibitin bayan rahoto na sirri da su ka samu cewa an yi safarar bata gari da su ka buya a cikin asibitin."

Ya bayyana cewa har su ka bar wurin, jami'an tsaro su na ci gaba da sintiri saboda samun labarin cewa akwai wasu daga cikin bata garin da su ka fantsama cikin gari.

'Yan sandan Kano sun yi shirin zabe

A wani labarin kafin yanzu, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta bari wasu jami’an tsaro irin su kungiyoyin bijilanti da jami’an KAROTA su shiga rumfunan zabe ba.

Kara karanta wannan

An gano masu kudin da jami'an tsaro suka kama a hannun wakilin PDP a Kaduna

Wannan na daga cikin matakan da rundunar ta dauka yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kafa dokar hana zirga-zirga daga 12:00 na dare ranar Juma’a, 15 ga watan Agusta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng