Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama a Shari'ar Matawalle da Gwamnatin Zamfara
- An kwashi dogon lokaci ana shari'a tsakanin Bello Matawalle da gwamnatin jihar Zamfara kan kwato motoci a gidansa
- Kotun daukaka kara da ke zamanta a Sokoto ta kawo karshen shari'ar a wani zama da ta yi a ranar, 8 ga watan Agustan 2025
- A hukuncin da ta yanke, kotun ta tabbatar da hukuncin da Kotun tarayya ta yanke wanda ya yi watsi da bukatun da Matawalle ya nema
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Kotun daukaka kara da ke Sokoto ta yanke hukunci kan karar da Bello Matawalle ya shigar da gwamnatin jihar Zamfara.
Kotun tatabbatar da hukuncin kotun tarayya mai zamanta a Sokoto wanda ta yi watsi da karar da Bello Matawalle ya shigar kan batun cewa motocin gwamnati da ake zargin ya kwashe bayan ya sha kaye a zaɓen 2023 mallakinsa ne.

Asali: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Idris, ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello Matawalle ya yi rashin nasara a kotu
Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa kwamitin alkalai uku na kotun daukaka kara, karkashin jagorancin Mai Shari’a A.M. Talba a ranar 8 ga watan Agusta 2025, ya yi watsi da karar da Matawalle ya shigar.
Kotun ta bayyana a cikin hukuncinta a shari’ar da ake yi mai lamba CS//S/2024, cewa hukuncin kotun tarayya reshen Sokoto kan ikon ‘yan sanda na gudanar da bincike kan zargin aikata laifi da aka kai musu ya yi daidai.
Kotun ta kara bayyana cewa Matawalle ya kasa kawo gamsashshiyar hujja da za ta tabbatar da cewa shi ne mamallakin motoci 40 da aka kwato daga gidansa, don haka ba shi da hujjar da zai nuna cewa an take masa hakkin mallakar kadara.
Yadda aka yi shari'ar Matawalle da gwamnatin Zamfara
"A watan Yuni 2023, gwamnatin Zamfara ta ba tsohon gwamnan da mataimakinsa kwanaki biyar na aiki su mayar da duk motocin da aka sace."
"Duk da haka, duk kokarin kwato motocin ya ci tura, lamarin da ya sa gwamnati ta nemi umarnin kotu. Bayan kotu ta bayar da umarni, ‘yan sanda suka kwato motocin fiye da 40."
"Bayan kwato motocin, Matawalle ya garzaya kotun tarayya a Gusau, inda aka ba da umarni a dawo masa da su. Har ila yau, ya shigar da wata kara daban a kotun yana neman tabbatar da hakkinsa na mallakar kadara, ciki har da motocin da ake magana a kai."
"Sai dai gwamnatin Zamfara ta nemi a mayar da shari’ar zuwa reshen Kotun Tarayya na Sokoto."
"Kotun tarayya a Sokoto ta yi watsi da karar a watan Disamba 2023, ta ki amincewa da duk bukatun da Matawalle ya nema, wanda hakan ya tabbatar da cewa motocin kadara ce ta gwamnatin Zamfara."
"Matawalle bai gamsu da hukuncin ba, ya garzaya kotun daukaka kara."
"Amma a hukuncin da aka yanke a ranar Juma’a da ta gabata, Kotun daukaka kara ta tabbatar da dukkan hukuncin kotun taayya ta Sokoto, tare da tabbatar da cewa ‘yan sanda suna da ikon bincikar duk wani zargin aikata laifi da aka kai musu."
- Sulaiman Bala Idris

Asali: Facebook
Matawalle ya ba gwamnan Zamfara shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ba da shawara ga Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Matawalle ya bukaci Gwamna Dauda Lawal da ya sauya sheka daga jam'iyyarsa ta PDP zuwa jam'iyyar APC.
Tsohon gwamnan na Zamfara ya bayyana cewa ko kadan bai da matsala da Dauda Lawal, don ya dawo jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng