Assadus Sunnah Ya Ƙure Masu Sukarsa kan Zama da Turji, Ya Yi Rantsuwa da Allah
- Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya koka kan zargin da ake yi masa na zama da Bello Turji, ya ce aikinsa don maslahar al’umma ne
- Malamin ya yi rantsuwa da Allah cewa ba don wani abin duniya suke wannan aiki ba, inda ya jaddada cewa maslahar al’umma ce kawai
- Ya kalubalanci masu sukarsa su fito su rantse idan suna da hujja, ya kuma kara da cewa ko gida bai mallaka ba a Kaduna da yake zaune
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya tura kalubale ga masu sukarsa game da zama da Bello Turji.
Malamin ya koka kan yadda wasu ke tunanin wai suna yin haka ne saboda suna samun wani abu da ya shafi kuɗi.

Source: Facebook
Bello Turji: Assadus Sunnah ya kalubalanci masu sukarsa

Kara karanta wannan
Wata 1 da rasuwar Buhari, ma'aikatansa sun yi hawaye, sun fadi kyawawan halayensa
Assadus Sunnah ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, malamin ya ce shi kam ko gida bai da shi a Kaduna saboda damuwarsa ita ce maslahar al'umma.
Sheikh Assadus Sunnah ya yi rantsuwa da Ubangiji kan cewa suna yin wannan aiki ne saboda Allah ba don abin duniya ba.
Ya ce:
"Idan wannan aiki da muke yi ba muna yi ba ne saboda maslahar al'ummarmu ta zauna lafiya, Allah ya sani.
"Ni Musa Yusuf Assadus Sunnah idan wannan aiki ba don Allah mu ke yi ba sai don wani abin duniya ina rokon Allah duk wani abin da nake nema duniya da lahira ka da ya ba ni.
"Kuma daga ƙarshe ya haramta mani shiga aljanna a gobe kiyama."

Source: Facebook
Asadus Sunnah ya magantu kan son abin duniya
Malamin ya kalubalanci masu zarginsa kan lamarin da su fito su yi rantsuwa kamar yadda shi ma ya yi.
"Wanda kuma yake da tuhuma yana ganin wannan aiki da muke yi ba don maslaha muke yi ba, ba don al'umma su zauna lafiya ba, ina kalubalantarsa.
"Shi kuma ya fito ya rantse da Allah cewa wannan aiki ba don Allah muke yi ba saboda wani abu ne da muke samu ya sa muke yin aikin.
"Shi ma ya yi rantsuwa ya roki Allah idan wannan aiki don Allah muke yi Ubangiji ya haramta masa shiga aljanna."
Malamin musuluncin ya ce shi bai dauki abin duniya wani abu ba, a nan ne ya ce ko gida bai da shi a Kaduna.
Malamin ya ce idan don abin duniya ne da ya tara amma suna yi don maslahar al'umma su zauna lafiya.
Sheikh Asada ya soki Albaniy Gombe saboda Turji
Kun ji cewa Malam Murtala Asada ya mayar da martani mai zafi ga Sheikh Adam Muhammad Albaniy kan sukar sulhu da Bello Turji.
Asada ya ce ya sha ba jami’an tsaro bayanai har aka kai wa Bello Turji hari, lamarin da ya fusata rikakken dan bindigan matuka.
Ya bayyana cewa Bello Turji ya taba yin bidiyo yana masa barazana saboda bayanan da suka kai ga kisan mutanensa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
