Sauki Ya Fara Isowa ga Talakawa bayan Dangote Ya Canza Farashin Litar Fetur a Najeriya

Sauki Ya Fara Isowa ga Talakawa bayan Dangote Ya Canza Farashin Litar Fetur a Najeriya

  • Fetur ya fara sauka a gidajen man yan kasuwa da na kamfanin NNPCL musamman a Legas da sauran sauran sassan Najeriya
  • Hakan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan matatar Dangote ta yi ragin N30 a farashin da take sayar wa ya kasuwa a rumbun ajiya
  • Sai dai har yanzu wasu na ganin kamata ya yi farashin litar fetur ya dawo tsakanin N200 zuwa N500 idan ana so talaka ya samu sauki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legas - Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) tare da sauran dillalan mai sun rage farashin man fetur (PMS) a gidajen mai.

Wannan sauki da aka fara samu a gidajen mai na zuwa ne bayan da matatar Dangote ta rage farashin kowace lita ga yan kasuwa a rumbun ajiya.

Gidan man kamfanin NNPCL.
Hoton daya daga cikin gidajen mai na kamfanin NNPCL a Najeriya Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ce daga sama da ₦950 a ranar Talata, yanzu ana samun kowace litar fetur a ƙasa da ₦865, gwargwadon wurin da mutum ke zaune.

Kara karanta wannan

Abin farin ciki: Hauhawan farashin kaya ya sauka a Najeriya, an bayyana dalilin saukin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda farashin fetur ya sauka a gidajen mai

Binciken da aka yi a ranar Juma’a ya tabbatar da cewa kusan duka gidajen mai a Legas da Ogun sun rage farashin fetur zuwa kasa da ₦900.

A daya bangaren kuma gidajen man NNPCL sun rage farashin litar fetur daga kusan N955 zuwa ₦865 a Legas da ₦870 a Ogun.

Kamfanonin MRS da Ardova, abokan huldar matatar Dangote, suma sun rage lita zuwa ₦865 da ₦875 a Legas da Ogun a jiya.

Gidagen man Heyden na sayar da lita ₦890; Fatgbems, ₦882; Akiavic, ₦894; Asharami, ₦895; Rainoil, ₦875; yayin da NIPCO ke ₦890.

Wannan sauki ya yadu zuwa jihohin Arewa, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu sai dai ya fi sauran yankuna tsada saboda nisan jigila.

Matatar Dangote ta yiwa yan kasuwa ragi

A kwanakin baya, an yi hasashen cewa farashin mai zai sauka zuwa ƙasa da ₦900 bayan matatar Dangote ta rage farashin lita a rumbun ajiya daga ₦850 zuwa ₦820.

Kara karanta wannan

PDP ta sacewa magoya bayan Jonathan da Obi guiwa da aka kafa kwamitin karba karba

Wata sanarwa da Babban Jami’in Harkokin Watsa Labarai na Kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya sanya hannu ta tabbatar da saukar farashin.

Kamfanin ya ce a matsayinsa na mai bada gudummawa ga ci gaban ƙasa, zai tabbatar da isar da man fetur ba tare da katsewa ba.

Sai dai rage farashin da Dangote ya yi ne ya tilasta sauran dillalai, ciki har da NNPCL, su rage farashinsu a gidajen mai a fadin Najeriya, wanda hakan zai isa ga talakawa.

Gaidan mai a Najeriya.
Hoton yadda mutane ke fama da layi wajen sayen fetur a gidajen mai a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abin da yan Najeriya ke bukata a farashin fetur

Har yanzu, wasu ’yan Najeriya suna ganin dole farashin fetur ya koma tsakanin ₦200 da ₦500 a kowace lita idan ana so su samu saukin rayuwa.

Wani mazaunin Legas, Favour Samson.

“Ya kamata farashin kowace lita ya dawo tsakanin ₦200 zuwa ₦500, sannan za a ga tasirinsa a duka fannoni na tattalin arziki.
"Sayan lita kan ₦850 akwai tsada kuma tana ƙara hauhawar farashin kaya."

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

'Yan Najeriya sun rage sayen fetur

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar NMDPRA mai hakkin kula da harkokin fetur ta bayyana cewa 'yan Najeriya sun rage sayan mai a watan Yuni 2025.

Hukumar ta sanar da cewa sayan man fetur ya ragu a watan Yunin 2025 zuwa lita biliyan 1.44, idan aka kwatanta da watan Mayu.

Mai magana da yawun NMDPRA, George Ene-Ita ya ce an saba ganin 'yan kasar na sayen akalla lita miliyan 48 kullum, amma adadin ya ragu zuwa lita miliyan 38.94 a Yuni.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262