Kaduna: An Sanya Dokar Hana Zirga Zirga a Zaria da Wasu Kananan Hukumomi 3
- Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga a kananan hukumomi hudu daga karfe 12:00 na tsakar dare ranar Asabar
- Yan sanda sun dauki wannan matakin ne saboda zaben cike gurbi da INEC za ta gudanar a mazabun yan Majalisar Tarayya da na jiha
- Mai magana da yawun yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan ya bukaci mazauna Zaria, Chikun, Kajuru da Basawa su bi dokar sau da kafa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Rundunar ‘Yan Sandan Reshen Jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar haramta zirga-zirga a wasu yankunan kananan hukumomi hudu.
Yankunan da yan sandan suka kakaba dokar, su ne za a gudanar da zabukan cike gurbin yan majalisar tarayya da na jiha a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025.

Source: Twitter
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
An hana zirga-zirga a kananan hukumomi 4
Ya ce dokar haramta zirga-zirgar za ta fara ne daga ƙarfe 12:00 na dare ranar Asabar a kananan hukumomin Sabon Gari, Zariya, Chikun da Kajuru da Kaduna.
Kakakin ‘Yan sandan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren tsaro da aka dauka kafin zabukan cike gurbi a yankunan da abin ya shafa.
Ya ce rundunar ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaron jama’a, hana tada tarzoma, da tabbatar da gudanar da zabe cikin tsari da lumana.
Rundunar ta shawarci jama’a da su kiyaye kuma su bi wannan doka sau da kafa domin tabbatar da an yi zabe an kare cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
'Yan sanda sun fadi wadanda dokar ta hau kansu
DSP Mansir Hassan ya ce akwai wasu ma'aikata na musamman da aka tsame daga wannan doka, kamar likitoci da malaman lafiya, jami'an tsaro da sauran makamantansu.
Bugu da kari, kakakin yan sanda ya bukaci mazauna wadannan kananan hukumomi su kasance masu zaman lafiya tare da bai wa jami'an tsaro hadin kai.
A cewarsa, hada kai tsakanin jami'an tsaro da fararen hula zai taimaka wajen tabbatar da an gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.

Source: Getty Images
Mazabun da INEC za ta gudanar da zabe a Kaduna
Legit Hausa ta gano cewa hukumar INEC ta kasa za ta gudanar da zabukan cike gurbin dan Majalisa mai wakiltar Chikun/Kajuru a Majalisar Wakilai ta kasa gobe Asabar
Sai kuma mazabar yan Majalisar dokokin jihar Kaduna biyu a za yi zaben cike gurbin, wanda suka hada da Zaria da kewaye, da mazabar Basawa, in ji rahoton Vanguard.
Wani dan kasuwa a Basawa, Zaria, Abdul Suleiman ya tabbatar wa Legit Hausa cewa ba zai fita shagonsa ba kuma ba shi da niyyar zuwa ya yi zabe.
Ya ce yana fatan a yi zabe lafiya a tashi lafiya, tare da addu'ar Allah Ya zaba masu shugabanni nagari.
"Na san za a sa wannan dokar, tun jiya na fada wa masu zuwa wurina ranar Asabar cewa ba zamu bude shago ba, yau ina gida gaskiya, kuma ban kai ga fita zabe ba.

Kara karanta wannan
Zabe ya dauki zafi, ana zargin an sace yar takarar majalisar tarayya da wasu 25 a Kaduna
"Muna fatan a yi zaben lafiya a tashi lafiya, dama burinmu Allah Ya kawo mana shugabanni masu tausayinmu," in ji ahi.
'Yan sanda sun haramta zirga-zirga a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana haramta zirga zirga a yayin da ake gudanar da zaben cike gurbi a wasu kananan hukumomi.
Kakakin yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa ya ce wannan doka za ta fara daga 12 na dare har zuwa ƙarfe 6:00 na yamma ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, domin tabbatar da tsaro da bin doka.
Za a gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Ghari/Tsanyawa don maye gurbin marigayi dan majalisar NNPP da ya rasu da kuma wasu rumfuna a mazabar Bagwai/Shanono.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

