Abin Farin Ciki: Hauhawan Farashin Kaya Ya Sauka a Najeriya, an Bayyana dalilin Saukin
- Hukumar kididdiga ta NBS ta fitar sabuwar sabarwa kan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya
- Hukumar ta ce farashin kayayyakin ya ragu zuwa kashi 21.88 a watan Yulin 2025, daga 22.22% a watan Yuni
- Rahoton ya nuna wannan shi ne karo na hudu a bana da aka samu raguwar hauhawar farashi, duk da ƙaruwa tsakanin wata da wata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar da sanarwa game da alkaluman hauhawar farashin kaya a Najeriya.
Hukumar ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 21.88 cikin 100 a watan Yuli 2025, daga 22.22 cikin ɗari a Yuni.

Source: Getty Images
NBS ta ce an samu saukin farashin abinci
Wannan adadi, da ke cikin rahoton 'Consumer Price Index (CPI)' da aka fitar a ranar Juma’a ya nuna faduwar farash a Najeriya, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne karo na hudu a bana da aka samu raguwar hauhawar farashi a kasar da ke fama da matsalar tattalin arziki.
A cewar NBS, hauhawar farashin watan Yuli ya nuna “raguwar kashi 0.34 idan aka kwatanta da hauhawar farashin watan Yuni 2025.”
Sai dai hukumar ta lura cewa, idan aka duba wata zuwa wata, hauhawar ta fi sauri a watan Yuli fiye da a watan Yuni.
Sanarwar ta ce:
“Idan aka kwatanta shekara da shekara, hauhawar farashin ta ragu da kashi 11.52 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Yuli 2024 (33.40%).
“A tsakanin wata da wata, hauhawar farashi a watan Yuli 2025 ya kai kashi 1.99, wanda ya fi na watan Yuni 2025 (1.68%) da 0.31%.
“Hakan na nufin cewa a watan Yuli 2025, ƙimar ƙaruwa a matsakaicin farashi ta fi ƙimar ƙaruwa a matsakaicin farashi a watan Yuni 2025."

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa

Source: Facebook
Ɓangaren da suka fi tasiri a saukar farashin kaya
Hukumar ta bayyana cewa abinci da abin sha marar giya, gidajen cin abinci da wuraren kwana, da harkokin sufuri sun fi taka muhimmiyar rawa a ƙididdigar bana.
NBS ta ce, a watan Yuli 2025, hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 22.74 bisa ɗari a shekara zuwa shekara, ya karu daga kashi 21.97 bisa ɗari.
Ta ce:
“Hakan ya faru ne saboda raguwar farashin wasu kayayyaki kamar kayan lambu, wake fari, shinkafa ta gida, garin masara, dawa, garin alkama, gero, da sauransu.”
Rahoton ya kuma nuna cewa matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na shekara guda, daga watan Agusta 2024 zuwa Yuli 2025, ya kai kashi 26.97 bisa ɗari, TheCable ta ruwaito.
Gwamnatin tarayya ta raba hatsi a Najeriya
Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta karyata cewa akwai tsananin matsin tattali da yunwa a Najeriya, tana mai cewa abin bai yi muni haka ba.
Mai ba shugaban kasa shawara wajen sadarwa, Sunday Dare ya bayyana cewa gwamnati ta fitar da ton 42,000 na hatsi da aka raba wa jihohi.
Da yake magana kan farfadowar Naira, Dare ya ce shirye-shiryen gwamnati da dama sun kare 'yan kasar daga yunwa da tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng

