Kano: 'Yan Sanda Sun Hana KAROTA da Sauran Hukumomin Tsaro Zuwa Filin Zabe
- Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana haramta zirga zirga a yayin da ake gudanar da zaben cike gurbi a wasu kananan hukumomi
- SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Kakakin rundunar ne ya bayyana haka a sakon da ya fitar kan shirin da ake na zaben lami lafiya a jihar
- Ya kuma bayyana cewa ba za a amince da hukumomin tsaro na jiha su karasa rumfunan zaben da zai gudana a ranar Asabar ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta bayyana cewa jami’an tsaron jihar, irin su kungiyoyin bijilanti da jami’an KAROTA, ba za su shiga rumfunan zabe ba.
Wannan na daga cikin shirin da ake gudanar wa don zabukan cike-gurbi da za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, a kananan hukumomi uku.

Asali: Facebook
A sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce an kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 12 na dare ranar Juma’a, 15 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan doka tana nan har zuwa ƙarfe 6:00 na yamma ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, domin tabbatar da tsaro da bin doka a zaben a fadin Kano.
'Yan sandan Kano sun shiryawa zabe
The Guardian ta ruwaito cewa za a gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Ghari/Tsanyawa don maye gurbin marigayi dan majalisar NNPP da ya rasu.
Haka kuma, za a sake gudanar da karin zabe a rumfunan zabe 10 na mazabar Bagwai/Shanono domin kammala sakamakon da aka fara tattara wa a baya.

Asali: Facebook
SP Kiyawa ya ce motocin daukar marasa lafiya, motocin kashe gobara, da na jami’an zabe da masu sa ido da hukumar INEC za su samu izinin zirga-zirga a lokacin zaben.
Rundunar ‘yan sanda Kano ta yi gargadi
Kiyawa ya gargadi cewa an haramta daukar makamai a lokacin zabe, sannan an hana sanya tufafi ko daukar kayayyaki masu dauke da tambarin jam’iyyun siyasa a rumfunan zabe ba.
Ya ce:
“Wadanda za su shiga rumfunan zabe su ne kawai wadanda suka cancanci kada kuri’a. Ba za mu lamucni masu yawon banza a rumfunan zabe ba za a lamunta ba."
Ya kuma kara da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da aiki da kware wa da bin doka a yayin aikin su, tare da tabbatar da zaman lafiya a duk lokacin da ake gudanar da zabukan.
'Yan sanda: 'Yan siyasa sun yi yarjejeniya a Kano'
A wani labarin, mun wallafa cewa shugabannin jam’iyyun siyasa a jihar Kano sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya a wani yunkuri na tabbatar da gudanar da zaben cike-gurbi lafiya.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata, 12 ga Agusta, 2025, a yayin taron masu ruwa da tsaki da rundunar ’yan sanda ta shirya a hedikwatarta da ke Bompai, Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng