Tsohuwar Hadimar Buhari Ta Rubuta Masa Wasika a Kabari, Ta Fadi Yadda APC Ta Lalace

Tsohuwar Hadimar Buhari Ta Rubuta Masa Wasika a Kabari, Ta Fadi Yadda APC Ta Lalace

  • Tsohuwar hadimar Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta rubuta wasika ga marigayin bayan wata daya da rasuwarsa
  • Lauretta Onochie ta yi kukan yadda APC ta rasa adalci, gaskiya da nagartar da marigayin ya tsaya kai lokacin yana kan mulki
  • Duk da korafe-korafenta, Madam Onochie ta ce mabiyan shugaba Buhari ba za su bar koyarwarsa ta gaskiya da rikon amana ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Bayan wata daya da rasuwarsa, ana ci gaba da tunawa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Tsohuwar Mai Bai wa Shugaba Muhammadu Buhari Shawara kan Harkokin Sada Zumunta, Lauretta Onochie, ta rubuta wasika mai cike da damuwa ga marigayi tsohon shugaban.

Tsohuwar hadimar Buhari ta tuna alherinsa a baya
Lauretta Onochie tare da Buhari a fadar shugaban kasa. Hoto: @Laurestar.
Asali: Twitter

Lauretta Onochie ta tuna kyawawan akidun Buhari

A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na X, ta yi ikirarin cewa APC yanzu ta zama “jam'iyya ta kashin kai” da aka mayar da hankali kan son rai.

Kara karanta wannan

"Ba gudu, ba ja da baya," Naja'atu ta karfafa gwiwar tambuwal bayan kamen EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onochie ta bayyana takaici kan yadda jam’iyyar APC ta lalace tun bayan barin Buhari mulki, tana cewa an watsar da adalci, gaskiya da rikon amana da aka santa a kai.

Onochie ta kara da cewa babu adalci ko daidaito, inda ta yi amfani da kalmar gargajiya “kpaied” wacce ke nufin an watsar da manufofinta gaba daya.

Lauretta Onochie ta koka kan yadda APC ta koma
Lauretta Onochie ta yaba da akidar da Buhari ya bari a APC. Hoto: @Laurester.
Asali: Twitter

Onochie ta fadi yadda manyan APC suka koma

Onochie ta soki yadda manyan jam’iyyar ke aikata laifi irin su cin zarafin ma’aikatan filin jirgi, da sace kudade sannan a basu mukaman jakadanci.

A cewarta, laifuffka a jam’iyyar yanzu ana lullube su da kyan gani da kamshi, muddin ba ka cikin adawa, komai za ka yi za ka tsira.

Duk da wannan damuwa, ta tabbatar wa marigayin Buhari cewa mabiyansa za su ci gaba da rikon koyarwarsa ta gaskiya da rikon amana.

Onochie ta koka kan halin da APC ke ciki

Lauretta Onochie ta ba Baba hakuri inda ta ce a yanzu babu APC saboda ta rasa adalci, ta gode masa saboda nuna yiwuwar samun nagarta a Najeriya da cikin ‘yan kasar.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

"Ka yi hakuri Baba babu APC a yanzu, mun gode maka da ka nuna mana cewa Najeriya za ta gyaru kuma har yanzu komai mai yiwuwa ne, Allah ya maka rahama."
“Shugabannin APC suna dukan ma’aikatan filin jirgi. Suna kwace jirage sannan a ba su mukamin jakadu. Ana boye mugunta da kyawawan kalmomi, sai dai idan kana adawa."

Ta kammala rubutunta da addu’ar Allah ya yi wa Buhari rahama, tare da tabbatar da cewa gaskiya za ta ci gaba da rayuwa duk da lalacewar siyasa.

Ma'aikatan Buhari sun tuna alherin marigayin

Kun ji cewa m’aikatan gidan tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a Daura sun yi jimamin rasuwar mai gidansu bayan wata daya.

Ha ila yau, ma'aikatan sun tuna kyawawan halayen marigayin inda suka ce kewayen gidan ya yi shiru tun bayan rasuwarsa wanda suka shiga wani hali.

Sun bayyana shi a matsayin mai tausayi, aboki, kuma mai ziyartar iyalansu, inda ya ba su kulawa da goyon baya da yake raye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel