Tashin hankali: 'Yan bindiga Sun Kutsa Gidan Sarki da Tsakar Dare, Sun Sace Ƴaƴansa
- Hankula sun tashi bayan yan bindiga sun kai wani hari a gidan Sarki inda suka sace ƴaƴansa guda uku yayin farmakin
- Lamarin ya faru ne a garin Gamalegi da ke Lafiagi a jihar Kwara a ranar Alhamis, da misalin ƙarfe 2:30 na dare
- Shugaban ‘yan sa-kai na Gbugbu, Suleiman, ya ce maharan sun shigo gidan Alhaji Hassan suna harbi, suka tafi da Aliyu, Sheshi da Ibrahim
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Yan bindiga sun dagawa al'umma hankali da tsakar dare bayan wani hari a cikin gidan Sarki a jihar Kwara.
’Yan bindiga dauke da makamai sun sace ’ya’yan Dagacin garin Gamalegi a karamar hukumar Lafiagi, jihar Kwara.

Source: Original
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga: Halin da Kwara ke ciki a yanzu
Jihar Kwara na daga cikin jihohin Arewa ta Tsakiya da ke fuskantar hare-haren yan bindiga a Najeriya bayan Benue da Nasarawa.
Ko a kwanan ma, miyagu sun kai wani mummunan hari ofishin rundunar yan sanda a jihar wanda ya ta da hankalin al'umma.
'Yan bindiga 200 dauke da makamai sun kai farmaki garin Babanla, jihar Kwara, inda suka kashe dan sanda tare da kwace bindigarsa.
ASP Adejumo Wasiu ya rasa ransa a harin da 'yan ta'addar suka kai ofishin ‘yan sanda na Babanla, kafin su farmaki kasuwar garin.

Source: Twitter
Yadda aka sace ƴaƴan Sarki a Kwara
Shugaban ’yan sa-kai na Gbugbu, Mista Suleiman, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:30 na safe, lokacin da suka kai hari suna harbi.
Ya bayyana cewa ’yan bindigar sun shiga gidan shugaban gari, Alhaji Hassan, suka tafi da ’ya’yansa uku, Aliyu mai shekara 15, Sheshi mai shekara 17, da Ibrahim mai shekara 14.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji sun babbake yan bindiga fiye da 100 a Zamfara, an yada hotuna
A cewarsa, ’yan sa-kai, sojoji, ’yan sanda da mafarauta sun tashi tsaye suka fara shiga daji domin ceto waɗanda aka sace da kuma kama masu laifi.
Ya ƙara da cewa, aikin zakulo maharan a dajin da neman waɗanda aka sace yana ci gaba a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.
Wane martani jami'an tsaro suka yi?
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, babu wani martani daga hukumomi ko kuma jami'an tsaro a jihar kan abin takaici da ya faru.
Sai dai mutane da dama a yankin na cikin fargaba duba da hare-haren yan bindiga da ke damunsu lokaci zuwa lokaci.
Yan bindiga sun yi wa Sarki tambayoyi a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa an saki Sarkin Yankuzo, Alhaji Babangida Kogo, bayan Ado Aliero ya tabbatar da bai da hannu a farmakin da aka kai masa.
Yan bindigar sun yi zargin Sarkin ne ya ba sojoji bayanan sirri da suka haddasa kisan ‘yan ta’adda sama da 30 suna bikin aure.
Rahotanni sun tabbatar da cewa babu kudin fansa da aka biya, an ce sun masa tambayoyi na sa’o’i kafin su yarda da cewa bai da alaka da harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
