Bello Turji Ya Mika Wuya ga Sojojin Najeriya? Hedikwatar Tsaro Ta Yi Bayani
- Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta fito ta yi bayani kan rahotannin da ke cewa tantitin dan bindiga, Bello Turji, ya mika wuya
- DHQ ta bayyana cewa hatsabibin dan bindigan bai ajiye makamansa ba, domin har yanzu sojoji na ci gaba da farautarsa ba
- Hakazalika, DHQ ta musanta cewa dakarun sojoji suna yin kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan batun ajiye makaman hatsabibin dan bindiga Bello Turji.
Hedkwatar tsaro ta kasa ta karyata rahotannin da ke cewa Bello Turji, ya mika wuya ga sojoji.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ce daraktan harkokin yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin wani taron bayani kan ayyukan rundunar sojojin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Bello Turji bai ajiye makamai ba' - DHQ
Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana cewa ko kadan Bello Turji bai ajiye makamansa ba.
“Amsar mai sauki game da jagoran ‘yan ta’adda, Bello Turji; Turji bai miƙa wuya ba, har yanzu muna ci gaba da farautarsa."
- Manjo Janar Markus Kangye
Bello Turji wanda ake nema ruwa a jallo, shi ne jagoran ‘yan bindiga da ke yin ayyuka musamman a jihohin Zamfara da Sokoto.
Ana zargin Bello Turji da kitsa hare-hare da dama kan al’ummomi a yankin Arewa maso Yamma.
Kwanan nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa jagoran ‘yan bindigan ya ajiye makamai tare da sako mutum 32 da aka yi garkuwa da su, bayan wani shirin sulhu.
DHQ ta musanta cewa sojoji na yin kisan gilla
Manjo Janar Markus Kangye ya kuma yi watsi da zarge-zargen kisan gilla da ake yi wa sojoji a yankin Kudu maso Gabas, yana mai cewa ba su da tushe, rahoton The Cable ya tabbatar.
Yayin da yake mayar da martani ga rahoton da Amnesty International ta fitar, Kangye ya ce sojoji ba sa aikata abin tashin hankali.

Asali: Facebook
"Me kuke nufi da kisan gilla? Shin sojoji za su ɗauki makamai su fita titi su fara harbin mutane? Kun san abin da Amnesty International ke yi. Kun san irin abubuwan da suke wallafawa."
"Kamar yadda na kan faɗa, duk wanda ke da waya a hannunsa na iya zama tushen samun labari ga duniya baki ɗaya."
“Amma zan iya gaya muku cewa sojoji ba sa aikata kisan gilla a Kudu maso Gabas."
- Manjo Janar Markus Kangye
Yaran Bello Turji sun kai hari
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ke biyayya ga Bello Turji, sun kai hari a kan wata hanya da ke jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun kai harin ne a kan hanyar Isa zuwa Shinkafi a jihar Sokoto, inda suka kashe wani matafiyi wanda bai san hawa ba, bai san sauka ba har lahira
Miyagun 'yan bindigan sun tare hanyar da babura sannan suka bude wuta kan motocin da ke wucewa wadanda ke dauke da mutane a cikinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng