Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya Amince da Kafa Sababbin Jami'o'i 9 a Kaduna da Wasu Jihohi 7
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i tara masu zaman kansu a jihohi takwas a Najeriya
- Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana haka jim kadan bayan taron Majalisar Zartarwa (FEC) a fadar shugaban kasa ranar Laraba
- Ya ce Gwamnatin Tinubu ta gaji takardun neman kafa makarantun gaba da sakandire sama da 500 amma yanzu an kawo sababbin ka'idoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kafa sabbin jami’o’i tara masu zaman kansu watau na kudi.
Wannan mataki dai ya kara yawan cibiyoyin ilimi na gaba da sakandire da ke hannun ‘yan kasuwa zuwa matakin da ba a taba gani ba.

Source: Twitter
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya sanar da amincewa da kafa sababbin jami'o'in a ranar Laraba, 13 ga watan Agusta, 2025, rahoton Tribune Nigeria.

Kara karanta wannan
Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alausa ya ce an amince da bai wa jami'o'in kudin lasisi ne a taron majalisar zartarwa ta kasa (FEC) da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja.
Jerin sunayen sababbin jami'o'in 9 na kudi
Da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, ministan ya jero sababbin jami’o’in da aka ba lasisi kamar haka:
1. Jami’ar Tazkiyah a Jihar Kaduna
2. Jami’ar Leadership a Abuja
3. Jami’ar Jimoh Babalola a Jihar Kwara
4 Jami’ar Bridget, Mbaise a Jihar Imo
5. Jami’ar Greenland a Jihar Jigawa
6. Jami’ar JEFAP a Jihar Neja
7. Jami’ar Azione Verde a Jihar Imo
8. Jami’ar Unique Open a Jihar Legas
9. Jami’ar American Open a Jihar Ogun.
Gwamnatin Tinubu ta kawo sauye-sauye
Tunji Alausa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaji bukatu 551 na neman kafa makarantun gaba da sakandire, ciki har da jami’o’i, da ke jiran izini.
A cewarsa, an sake duba wadannan bukatu tare da tsaurara ka’idoji, wanda ya rage su zuwa 79, inda daga ciki aka amince da guda tara a ranar Laraba.
“Saboda rashin aiki yadda ya kamata a hukumar NUC ne ya kawo jinkirin ba da lasisin kafa makarantun.
"Tun da muka zo muka kawo sauye-sauye domin saukaka tsarin kuma amince da kafa wadannan jami'o'i ma daga cikin sakamakon gyaran da muka yi," in ji shi.

Source: Twitter
Ministan ya kara da cewa da dama daga cikin jami’o’in da aka amince da su yanzu tuni sun fara gina makaranta kuma sun zuba biliyoyin Naira suna jiran samun sahalewar aiki.
Ya kara da cewa gwamnati ta kafa dokar dakatar da karbar bukatu na kafa jami’o’i, kwalejojin ilimi da na fasaha na kudi, sai wadanda suka cika sababbin ka’idojin gudanarwa, in ji Leadership.
ASUU ta yi barazanar rufe jami'o'in gwamnati
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta yi gargadin shiga yajin aiki saboda gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta dauka.
ASUU ta koka kan halin da mambobin ta ke ciki, tana mai cewa malamai na koyar da dalibai cikin yunwa, saboda rashin wadataccen albashi da alawus.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki cikin gaggawa don kauce wa yajin aikin da ke tunkaro jami’o’i.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
