'Yan Sanda: "'Yan Siyasa a Kano Sun Yi Alkawarin Hana Zubar da Jini a Zaben Cike Gurbi"

'Yan Sanda: "'Yan Siyasa a Kano Sun Yi Alkawarin Hana Zubar da Jini a Zaben Cike Gurbi"

  • An gudanar da taron masu ruwa da tsaki a hedikwatar ‘yan sanda ta jihar Kano a Bompai da shugabannin jam’iyyun siyasa
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zabe ta kasa, INEC ke shirin gudanar da zabukan cike gurbi a ranar 16 ga Agusta 2025
  • Kwamishinan 'yan sanda na Kano, Ibrahim Bakori ya jaddada cewa ba za su sassauta wa duk wanda ya karya doka yayin zaben ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugabannin jam’iyyun siyasa a jihar Kano sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a wani yunkuri na tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana.

An sanya hannu a kan yarjejeniyar a yayin zaben cike-gurbi da za a gudanar ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025 da ke kara karato wa.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: PDP ta amince da bukatun Wike, an gano dalili

Yan sandan Kano da 'yan siyasa
'Yan sandan Kano sun zauna da 'yan siyasa kafin zaben cike gurbi Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan siyasa sun shiga yarjejeniya a Kano

A cewar Kiyawa, an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, Bompai, ranar Talata.

Ya ce sanya hannu a takardar za tq ƙarfafa zaman lafiya, tsaro, da bin dokokin zaɓe kafin da kuma yayin gudanar da zaben cike gurbi.

Ya ce:

“A yayin taron, dukkannin jam’iyyun da suka halarta sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, tare da shan alwashin gudanar da harkokin zabe ba tare da tashin hankali ba,"
“Domin shiryawa zaben cike gurbi a Ghari/Tsanyawa da kuma zaben cike-gurbi na Bagwai/Shanono, da za a gudanar ranar Asabar, 16 ga Agusta 2025, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta shirya taron masu ruwa da tsaki tare da ‘yan takara da shugabannin jam’iyyu daban-daban a yau, 12 ga Agusta 2025.”

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina, an ceto mutane

Shawarar Kwamishinan ‘yan sandan Kano ga ‘yan siyasa

Ya bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Bakori, ya umarci masu ruwa da tsaki da su kiyaye sharuddan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka samar.

Haka kuma, ya shawarce su da su gudanar da kamfen da duk abin da ya shafi zaben bisa ka’ida, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya doka ko tayar da hankula zai gamu da hukuma.

Jami'an rundunar yan sandan Kano
Rundunar yan sanda ta yi alkawarin tura isassun jami'ar zuwa rumfunan zabe Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kwamishinan ya tabbatar wa jama’a cewa za a tura jami’an tsaro yadda ya kamata a ranar zabe domin samar da yanayi mai aminci ga masu kada kuri’a da jam’iyyun siyasa su gudanar da harkokinsu.

Kano: Rundunar 'yan sanda ta kori kurtu

A baya, mun wallafa cewa Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sallami wani kurtu, Ado Abba, bayan korafe-korafen jama’a da suka zarge shi da karɓar na goro a kan tituna.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan ya ce shi kansa ya taɓa gamu wa da korarren jami’in yayin da yake tafiya a cikin motarsa.

SP Kiyawa ya ce kwamishinan ‘yan sandan Kano, Salman Dogo, ne ya bayar da umarnin korar tsohon kurtun da aka kammala bincike a kan zarge-zargen da aka shigar a kansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng