Hatsabibin Ɗan Bindiga Ya Hallaka Ɗan Uwansa bayan Korafin Jama'a kan Haraji

Hatsabibin Ɗan Bindiga Ya Hallaka Ɗan Uwansa bayan Korafin Jama'a kan Haraji

  • 'Dan ta'adda Kachalla Alti ya kashe dan bindiga Dankarami Usaini a Matsuki, Zamfara, bayan rikicin nuna iko tsakanin bangarorinsu
  • Rahotanni sun ce Dankarami ya dade yana azabtar da mazauna yankin, inda ake zargin yana karɓar haraji da tilasta kai hari
  • Bayan kisan, mazauna sun tsere saboda tsoron ramuwar gayya, lamarin ya jefa yankin cikin tashin hankali da jin karar harbe-harbe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Wani fitaccen dan bindiga ya yi ajalin wani hatsabibi kan rashin jituwa da ta faru a jihar Zamfara.

An tabbatar da cewa Kachalla Alti, ya kashe wani rikakken dan bindiga a Matsuki, karamar hukumar Tsafe a jihar.

Yan bindiga sun yi ajalin juna a Zamfara
An rage mugun irin bayan kashe dan bindiga a Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Rahoton Zagazola Makama ya ce rikicin ya faru ne kan kokarin nuna nuna iko bayan korafin al'umma kan karbar haraji.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun babbake yan bindiga fiye da 100 a Zamfara, an yada hotuna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake yawan samun rigima tsakanin 'yan bindiga

Wannan ba shi ne karon farko ba da yan bindiga ke kai hari kan junansu musamman kan kokarin nuna iko.

Maharan da kansu suke ragewa sojoji aiki wanda yake sanadin mutuwar wasu hatsabiban yan bindiga.

Wasu majiyoyi na cewa mafi yawan manyan yan bindiga na samun matsala da juna kan iko ko kokarin mamayar wasu yankuna a daji.

Kachallah Alti ya hallaka dan bindiga a Zamfara

Majiyoyi sun nuna cewa lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 4:45 na yamma a ranar Litinin, inda ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da gudu.

Shaidu sun bayyana cewa wanda aka kashe, Dankarami Usaini, mai shekaru 40, ɗan asalin Matsuki ne, yana zaune a dajin Dangajeru na tsawon lokaci.

Ana zargin Dankarami da azabtar da jama’a ta hanyar karɓar haraji da kai hari kan waɗanda suka ƙi amincewa da umarninsa a yankin.

Majiyoyi sun ce Dankarami ya shiga kauyen ne domin tattara kuɗin haraji a madadin Kachalla Alti, wanda ƙani ne ga Adamu Aliero.

Kara karanta wannan

'Mun yi rashi': Aminu Ado ya kadu bayan mutuwar ministoci 2 a hatsarin jirgi

Rigima a tsakanin yan bindiga ta yi ajalin dan ta'adda
Kachallah Alti ya hallaka dan bindiga, Dankarami. Hoto: Legit.
Asali: Original

Zargin da ke kan Dankarami a Zamfara

Sai dai mazauna sun daɗe suna nuna rashin jin daɗi kan “tsananin cin zarafi” da Dankarami yake musu, inda suka nemi Alti ya shiga tsakani.

Kachalla Alti ya isa kauyen tare da yaransa, inda ya harbe Dankarami har lahira nan take, lamarin da ya girgiza mazauna.

Bayan kisan, mutane da dama suntsere zuwa makotan kauyuka saboda tsoron ramuwar gayya daga magoya bayan Dankarami Usaini.

Majiyoyin yankin sun bayyana cewa har yanzu akwai tashin hankali, inda aka ci gaba da jin karar harbi a hanyoyin dajin kusa.

Sojoji sun babbake yan bindiga 100 a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa sojojin Najeriya sun gano gawarwakin yan bindiga fiye da 60 bayan luguden wuta kansu a Zamfara da ake kukan rashin tsaro.

Sama da babura 30 da makamai sun kone, fiye da ‘yan ta’adda 100 sun mutu a harin da aka kai wanda ya kara rikita yan ta'addan.

Rundunar ta ci gaba da farautar maboyarsu domin hana sake haduwarsu ko kai hari a cikin dazukan yankin da ke fama da matsalolin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.