Saudiyya, Amurka da Wasu Kasashe Za Su Shigo Najeriya, Za a Dauki Matasa Aiki
- Gwamnatin tarayya na ci gaba lalubo hanyoyin da za a samar da ayyukan yi domin rage zaman kashe wando tsakanin matasan Najeriya
- Ministan kwadago, Muhammad Maigari Dingyadi ta ce tattaunawa ta yi nisa da Saudiyya, Birtaniya, Amurka da wasu kasashe don daukar yan Najeriya aiki
- Muhammad Maigari Dingyadi ya ce tuni gwamnati ta rattaba hannu a yarjejeniya da kasa daya, sauran kuma an kusa karkare tattaunawa da su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tattaunawa ta yi nisa da Saudiyya, Birtaniya, Amurka, Australia, da wasu ƙasashe domin samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya.
Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja ranar Talata.

Source: Facebook
A cewar ministan, wannan shiri na daga cikin tsare-tsaren gwamnati na magance matsalar rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakanin matasa, in ji Leadership.

Kara karanta wannan
'Mun yi Allah wadai': Atiku ya fadi 'gaskiyar' abin da ya sa EFCC ta tsare Tambuwal
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya za ta hada kai da Saudiyya da wasu kasashe
Dingyadi ya bayyana cewa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da wata ƙasa, yayin da tattaunawa da sauran ƙasashen ta kai matakin karshe.
Ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da yanayin aiki mai aminci, adalci, da gasa.
Sannan ya ce gwamnatin tarayya za ta yi amfani da sauye-sauyen da take yi a cikin gida da haɗin gwiwar ƙasashen waje don ƙara yawan ayyukan yi ga yan Najeriya.
Yadda ake kokarin samar da ayyuka a Najeriya
Muhammad Dingyadi ya ce:
“Ba wai muna horar da ’yan Najeriya ne kawai don su tafi ƙasashen waje ba, muna horar da su ne domin su wakilci ƙasarmu yadda ya dace, sannan mu tabbatar cewa muna amfana da aikinsu a waje, ta fuskar kuɗi da sauran fannoni.”
"Wannan shiri ne da za mu amfanar da juna, yayin da muke tura ƙwararrun ’yan Najeriya zuwa waje, wasu daga cikin yan kasashen wajen za su zo nan, riba ce ta bangarorin biyu.”

Source: Twitter
Nasarorin Ministan kwadago a watanni 9
Da yake bayani kan watanni tara da ya shafe a ofis, Dingyadi ya ce ma’aikatarsa ta samu kwanciyar hankali a tsakanin ma’aikata sai dai yajin aikin gargadi da malaman jinya suka yi kwanan nan.
Ya danganta wannan nasara da inganta yanayin tattaunawa, sauraren damuwar ma’aikata, da kuma ƙarfafa haɗin kai da ƙungiyoyin ƙwadago.
Ministan ya kara da cewa an fadada shirye-shiryen koyon sana’o’i, inda aka horas da ’yan Najeriya da dama a fannoni daban-daban.
Dubban ma'aikata na fuskantar kora a Najeriya
A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta gargadi wasu ma'aikata 3,598 kan rashin halartar tantancewar da ta shirya masu a watan Agusta, 2025.
Wadannan ma'aikata dai ba su halarci tantancewar da gwamnati ta shirya ba a shekarar 2021, lamarin da ya sa aka fara zargin suna amfani da takardun daukar aiki na bogi.
Hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya ta sake sanya lokacin tantancewa, ta ce duk wanda bai halarta ba ya rasa aikinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
