EFCC Ta 'Tona Asirin' Ƴan Siyasa, Ta Faɗi Yadda ake Shirya Sata kafin Shiga Ofis
- Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta ce wasu ‘yan siyasa na bayyana kadarorin da ba su mallaka ba kafin su hau mulki
- Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya bayyana yadda aka gano wani babban gida da aka rubuta a wurin da bai wanzu ba
- EFCC ta shawarci CCB ta tsaurara binciken da take yi kan irin wannan dabarar da ake yi domin satar dukiyar al'umma
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta bayyana cewa wasu ‘yan siyasa sun ƙirƙiri wata sabuwar dabara domin ci gaba da yin sata.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar ranar Talata da hadin gwiwar Hukumar Da'ar Ma'aikata (CCB).

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Olukoyede ya ce wasu ‘yan siyasa na bayyana kadarorin da ba su mallaka ba kafin su hau kujerar mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, wannan dabara ta zama hanyar satar dukiya tun kafin a hau kujerar mulki domin gujewa bincike daga hukumomi.
Yadda EFCC ta gano dabarar ‘yan siyasa
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Olukoyede ya ce hukumar ta gano cewa wani mutum da ake bincike ya yi amfani da lambar gida daban a takardar bayyana kadarorinsa.
Ya ce:
“Akwai wani lamari da muka bincika. Na ce wa tawagata, ku samo fam ɗin CCB ku duba shi. Na lura akwai abin da ban gamsu da shi ba a rahoton. Mun duba fam ɗin CCB, mu ka gano daya daga cikin manyan kadarori masu darajar sama da Naira biliyan uku, amma lambar wurin daban take da ainihin wurin. Wannan ya sa muka zurfafa bincike.”
Olukoyede ya ce binciken EFCC ya gano cewa dukiyar da aka bayyana a fam ɗin babu ita a lokacin da aka bayyana cewa an mallaki kadarar.
Amma bayan mutumin ya lashe zaɓe, kafin a rantsar da shi, sai ya bayyana wani gida mai lamba lamba 39 a wata unguwa, amma a binciken EFCC an gano asalin gidan yana lamba 44.
Ana zargin cewa ana yin shirin sata ne tun kafin a rika madafun iko, bayan an shiga ofis sai a mallaki kadarorin da ba za a binciki yadda aka same su ba.
Shugaban EFCC ya shawarci Hukumar CCB
Shugaban EFCC ya shawarci Hukumar Kula da 'Da'ar Ma’aikata (CCB) da ta yi taka-tsantsan da irin wannan dabarar da ‘yan siyasa ke amfani da ita don kauce wa bincike.

Asali: Facebook
“Yanzu, suna bayyana abin da suke shirin saye lokacin da za su samu mulki tun kafin a rantsar da su. Wannan abin takaici ne sosai. Mun ga hakan, mu ka ce wannan lamarin ya yi muni matuƙa.”
A nata jawabin, Shugabar Ma’aikata ta Tarayya, Didi Esther Walson-Jack, ta ce an ƙaddamar da wani sabon tsarin ne domin inganta ɗa’a a ma’aikatar gwamnati tare da dakile cin hanci.
EFCC ta yi martani ga jam'iyyar ADC
A baya, kun ji cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta karyata zarge-zargen da jam’iyyar ADC ta yi mata a yakin da ta ke da rashawa.
Shugaban hukumar Ola Olukoyede ne ya musanta zargin, tare da bayyana cewa jam’iyyar hamayya ta ADC na ƙoƙarin siyasantar da binciken da ta ke gudanarwa.
Shugaban ya ƙaryata ikirarin jam’iyyar cewa gayyatar da hukumar ta yi wa wasu manyan ‘yan adawa a kwanakin baya ta dogara ne wasu dalilan siyasa ko alaka da APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng