Bayan Yada Jita Jitar Mutuwar Tinubu a Daren Jiya, Hadiminsa Ya Fadi Gaskiya
- A daren Talata, an yada jita-jitar rashin lafiyar Shugaba Bola Tinubu, wasu ma suna cewa ya rasu, duk ba tare da hujja ba
- Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce labaran karya ne, yana mai jaddada cewa Tinubu yana cikin koshin lafiya
- Abdulaziz ya ce wasu sun gana da Tinubu a Abuja a daren Talata, ciki har da dan majalisa Abdulmumini Jibrin daga Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - A ranar Talata 12 ga watan Agustan 2025 an yi ta jita-jitar cewa rashin lafiyar Bola Tinubu ta yi tsanani.
Akwai wadanda har cewa suke yi shugaban ya rasa ransa duk da cewa mafi yawansu a fakaice suke yi ba su fito fili sun fada ba.

Asali: Facebook
Hadimin Tinubu ya tsage gaskiya kan jita-jita

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki
Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz ya yi karin haske yayin hira da DCL Hausa da aka wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdulazizi ya ce wannan abin dariya ne saboda mutane suna aminta da jita-jita da ake yadawa kan abin da ba gaskiya ba.
Hadimin ya ce kowa ya sani babu wani mutum da ya fi karfin rashin lafiya ko mutuwa saboda Allah babu abin da ba zai yi ba.
Ya ce:
"Dariya abin yake ba mu domin mun san abin da ake fada ba haka ba ne, na biyu akwai abin takaici na cewa mutane suna son jin labarin bogi.
"Shugaban kasa kamar ko wane mutum, kamar ni da kai dan Adam ne zai iya rashin lafiya, zai iya mutuwa ita ciwo ko mutuwa ba a tsufa take ba kuma mutuwa ba a ciwo take ba.
"Mai lafiya idan Allah ya ga dama sai ya karbi abinsa ko kuma marar lafiya Allah ya tayar da shi."

Asali: Facebook
Mutanen da Tinubu ya gana da su a Abuja
Abdulaziz ya ce ko a daren jita Talata akwai wadanda suka gana da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja kuma yana cikin koshin lafiya.
Har ila yau, ya ce a ranar Litinin dan majalisa daga jihar Kano, Abdulmumini Jibrin ya gana da Tinubu inda ya ce wannan ba abin magana ba ne.
Ya kara da cewa:
"Ko a daren nan akwai wadanda suka gan shi kuma akwai wasu manyan APC da suka gana da shi a daren Talata a Abuja.
"Kuma ko a jiya (Litinin) akwai wadanda suka gan shi, dan majalisa daga Kano, Abdulmumini Jibrin ya je suka yi ganawa na kusan awa biyu.
"Ban san ma mai zai kawo wannan jita-jita ba saboda ba abu ne wanda aka yi kwanaki ba a gan shi ba bare a yi ta magana."
Sanata ya fadi halin da Tinubu ke ciki
Kun ji cewa Sanata Orji Uzor Kalu ya yi karin haske kan rashin lafiyar shugaban kasa, Bola Tinubu da ake ta yadawa a Najeriya.
Sanatan da ya fito daga jihar Abia ya karyata jita-jitar cewa Tinubu yana cikin mummunan yanayi na rashin lafiya.
Ya ce ya yi magana da Tinubu ta waya kuma yana shirin tafiya Japan da Brazil domin wani taro mai muhimmanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng