Yadda 'Yan Bindiga Suka Shirya Kwanton Bauna a Zamfara, an Kashe Jami'an Tsaro
- An samu asarar rayuka bayan 'yan bindiga sun shirya harin kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihar Zamfara
- Lamarin ya jawo an samu asarar rayukan jami'an tsaro tare da fararen hular da aka ceto daga hannun 'yan bindiga
- 'Dan majalisar jiha mai wakiltar yankin da lamarin ya auku, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo musu dauki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - ’Yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton-bauna a kauyen Adabka, da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun hallaka akalla jami’an tsaro guda 10 da kuma fararen hula uku a yayin harin.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne a ranar Jumma’a lokacin da jami’an tsaro suka yi ƙoƙarin ceto mutane bakwai da aka sace a garin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro
Lamarin ya auku ne lokacin da jami’an tsaro ke komawa garin Adabka, bayan wani samame da ya kai ga kubutar da wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su.
Mazauna yankin sun ce waɗanda suka mutu sun haɗa da ɗan sandan Mopol guda daya, mambobin rundunar CJTF guda biyar da kuma jami'an rundunar Askarawan Zamfara guda hudu.
Haka kuma, fararen hula uku da aka ceto su ma an kashe su yayin kwanton-baunar.
Hakimin Adabka, Sarkin Kiyawa Adabka, Alhaji Nafi’u Shehu, ya ce wani ɗan sandan Mopol da aka yi zaton ya bace a lokacin harin ya dawo garin bayan ya kwashe kwanaki hudu cikin daji.
Ya ce jami’in ya gudu daga sansanin ’yan bindigan ne yayin da wasu daga cikinsu ke yin Sallah, wasu kuma suna barci.
Haka kuma, ya bayyana cewa har yanzu ba a samu gawarwakin jami’an tsaron da aka kashe ba domin yi musu jana’iza.
An bukaci gwamnati ta kawo dauki
Ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Bukkuyum ta Kudu Kudu, Hon. Hamisu A. Faru, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki domin kare rayukan al’ummomin mazabarsa.
Yayin da yake magana da manema labarai, ya ce mazauna mazabarsa na rayuwa cikin tsananin fargaba, musamman bayan kisan jami’an tsaron da ke kare su.
Ya ce wasu daga cikin sauran jami’an tsaron ma sun riga sun koma Zuru.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa kusan kaso 70% na yankin Bukkuyum ta Kudu yanzu yana ƙarƙashin ikon ’yan bindiga.

Source: Original
Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta tura jiragen yaƙi zuwa dajin Bukkuyum, inda ’yan ta’addar ke da sansani.
"Muna roƙon gwamnatin tarayya da ta tura ƙarin jami’an tsaro zuwa ƙaramar hukumar mu domin yakar ’yan ta’addan da ke addabar al’ummominmu, musamman a sassan Kudancin Bukkuyum."
- Hon. Hamisu A. Faru
'Yan bindiga sun kakaba haraji kan kauyuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun sanya haraji kan wasu kauyukan jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
'Mutane sun yi takansu': Halin da ake ciki a Borno bayan Boko Haram ta kashe sojoji
'Yan bindigan sun sanya harajin ne a kauyuka 35 na gundumar Dan Isa da ke karamar hukumar Kauran-Namoda.
Sun bayyana cewa sai mutanen kauyukan sun biya harajin kafin su ba su damar zuwa gonakinsu don gudanar da noma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

