Shugaba Tinubu Ya Yi Ruwan Mukamai a Hukumomin Tarayya Ana Jita Jitar Ciwo

Shugaba Tinubu Ya Yi Ruwan Mukamai a Hukumomin Tarayya Ana Jita Jitar Ciwo

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sababbin kwamitocin lura da aikin hukumar sadarwa ta NCC da asusun USPF
  • Idris Olorunnimbe ya zama shugaban majalisar NCC, yayin da Dr. Aminu Maida ya ci gaba a matsayinsa na mai gudanar da aikin hukumar
  • A gefe guda kuma Ministan Sadarwa, Dr. Bosun Tijani, zai jagoranci kwamitin USPF, asusun da ke samar da kudin ayyukan sadawara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa kwamitin gudanarwa na Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC).

Haka kuma ya amince da kafa kwamitin da Asusun Samar da Ayyukan Sadarwa (USPF), wanda ke ƙarƙashin ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki.

Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Tinubu ya yi sababbin nade nade Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wannan na kunshe a sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata da aka wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Da gaske ba shi da lafiya? Gwamna ya fadi halin da ya tarar da Shugaba Tinubu a Aso Rock

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi nade-naden hukumar NCC

Sanarwar ta ce Tinubu ya nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban majalisar da ke sa ido a hukumar NCC bayan ya rasa irin kujerar a UBEC.

Da farko shugaban kasa ya nada shi, amma sai ya canza shi da Sanata Tanko Al-Makura.

Dr. Aminu Maida ya ci gaba a matsayin shugaban da ke rike da hukumar sadarwar.

Shugaba Tinubu ya fara nada Dr. Maida a watan Oktoban 2023, kuma majalisar dattawa ta amince da shi a watan Nuwamba.

Olorunnimbe, tsohon jami'i ne a hukumar kula da Asusun Ƙirƙirar Ayyukan Yi ta Jihar Legas (LSETF), kuma ya yi fice wajen shirye-shiryen samar da ayyukan yi da bunƙasa kasuwanci ga matasa.

Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Tinubu ya yi nadi a NCC da USPF Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sauran jami'an hukumar NCC da aka haɗa da:

  1. Abraham Oshidami
  2. Rimini Makama
  3. Hajiya Maryam Bayi
  4. Col. Abdulwahab Lawal (Rtd)
  5. Sanata Lekan Mustafa
  6. Chris Okorie
  7. Princess Oforitsenere Emiko – Sakatariyar kwamitin

Kara karanta wannan

Shugabar FCC tana murnar Tinubu ya tsawaita wa'adinta, an sanar da korar ta daga ofis

Shugaba Tinubu ya yi nade-naden hukumar USPF

Shugaban ƙasa ya kuma amince da kafa sabon kwamiti ga hukumar USPF, tare da Ministan Sadarwa, Dr. Bosun Tijani, a matsayin shugaban kwamitin.

Sauran 'yan kwamitin USPF sun haɗa da:

  1. Idris Olorunnimbe – Mataimakin shugaban kwamitin
  2. Abraham Oshidami
  3. Rimini Makama
  4. Aliyu Edogi Aliyu – wakili daga FMCIDE
  5. Joseph B. Faluyi – wakili daga Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya
  6. Auwal Mohammed – wakili daga FMBNP
  7. Uzoma Dozie
  8. Peter Bankole
  9. Abayomi Anthony Okanlawon
  10. Gafar Oluwasegun Quadri – Sakatariyar USPF

An kafa USPF ne domin cika manufofin ƙasa na samar da damar sadarwa da fasahar bayanai ga yankunan karkara da ke sassan Najeriya domin su yi daidai da zamani.

An gano gaskiyar batun lafiyar Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa Fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da rahotannin da ake yada wa da ke cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana fama da rashin lafiya.

Ta ce shugaban ƙasa yana cikin koshin lafiya, duk da rahoton cibiyar ICIR da ya ce wasu majiyoyi sun bayyana ana shirin tura Tinubu ƙasar waje domin duba lafiyarsa cikin gaggawa.

Rahoton cibiyar ICIR ta ce majiyoyi sun tabbatar mata cewa shugaban ƙasa ya kwanta rashin lafiya tsawon wasu kwanaki, abin da ya sa bai halarci wasu manyan tarukan ƙasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng