'Yan Majalisa Sun Kai Karar Gwamna Dauda kan Matsalar Rashin Tsaro

'Yan Majalisa Sun Kai Karar Gwamna Dauda kan Matsalar Rashin Tsaro

  • Majalisar dokokin jihar Zamfara ta nuna damuwarta kan yadda 'yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka
  • 'Yan majalisar dokokin sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda Gwamna Dauda Lawal yake tafiyar da al'amuran tsaro
  • Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da gwamnan gefe, ta dauki matakan kawo karshen ayyukan 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Bashar Gummi, ta sake bayyana rashin jin daɗinta kan shirin Gwamna Dauda Lawal dangane rashin tsaro.

Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jagoranci harkokin tsaro a jihar domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

'Yan majalisar Zamfara sun taso Gwamna Dauda a gaba
Gwamna Dauda Lawal na shan suka daga 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce a zaman majalisar na ranar Talata, mambobi sun yi bayani dalla-dalla kan yadda ‘yan bindiga suka lalata jihar ta hanyar kai hare-hare a sassa daban-daban.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka shirya kwanton bauna a Zamfara, an kashe jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan majalisa sun koka da rashin tsaro

Mambobin sun zargi gwamnan da rashin kai ziyarar ta’aziyya, ko aika wakilai na gwamnati, ko kuma bayar da wata irin gudunmawa ga al’ummomin da abin ya shafa ko iyalan waɗanda aka kashe.

Yayin gabatar da kudirin neman daukar mataki kan lamarin, ɗan majalisa mai wakiltar Bukkuyum ta Arewa, Bashir Masama, ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen yaki da ‘yan bindiga.

Bashir Masama ya ce ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyuka huɗu da ke cikin mazabarsa, yana mai bayyana cewa al’ummar yankin na tserewa zuwa wasu wurare don samun tsira saboda matsalar tsaro.

Yayin goyon bayan kudirin, Bashir Zango, mai wakiltar Bungudu ta Yamma, ya ƙara da cewa kauyukan Gidan Bugaje, Zaman Gida, Kukan Nine da Gidan Dan-inna sun zama filayen yaki na ‘yan ta’adda, inda duk wanda ya kuskura ya shiga, kamar ya kai kansa ga hallaka ne.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

Ɗan majalisa mai wakiltar Maradun I, Faruk Dosara, ya soki gwamnatin jihar bisa zargin barin mutanensa a ‘yan bindiga.

Ya yi kira ga majalisar da ta yi la’akari da fara shirin aika wa gwamna takardar tsigewa saboda sakaci da kuma yin watsi da aikinsa baki ɗaya.

Zamfara: 'Yan majalisa sun soki aikin gwamna

Mambobin majalisar, yayin bayyana damuwarsu da takaicinsu game da gwamnatin jihar, sun roƙi gwamnatin tarayya da ta ɗauki cikakken ikon kula da harkokin tsaro a jihar.

Sun yi gargadin cewa muddin gwamnatin tarayya ba ta yi watsi da gwamnatin jihar da kuma ƙoƙarin gwamnan na hana jami’an tsaro yin aikinsu ba, ta kuma karɓi cikakken iko, yaki da ‘yan bindiga ba zai ƙare nan kusa ba.

'Yan majalisa sun caccaki Gwamna Dauda Lawal
Dauda Lawal ya ce samar da tsaro hakkin gwamnatin tarayya ne Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamna Dauda Lawal ya yi martani

A martaninsa kan wannan zargi, Mustafa Jafaru, mai taimakawa gwamna kan harkokin yada labarai da sadarwa, ya ce batun tsaro nauyin gwamnatin tarayya ne.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga a Bauchi, an kashe miyagu

Ya jaddada cewa duk wanda ya zargi gwamna da gazawa wajen tsaro a jihar, bai fahimci kundin tsarin mulki ba.

Sojojin sama sun soye 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta kai hare-hare kan 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Jiragen yakin rundunar sun yi ruwan wuta kan 'yan bindigan da ke halartar wani daurin aure a karamar hukumar Tsafe.

Hare-haren sun jawo an kone 'yan bindiga da dama yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng