EFCC Ta Yi Martani da Jam'iyyar ADC Ta Kira Ta 'Karen Farautar Tinubu'

EFCC Ta Yi Martani da Jam'iyyar ADC Ta Kira Ta 'Karen Farautar Tinubu'

  • Hukumar EFCC ta zargi ADC da ƙoƙarin siyasantar da aikinta na yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya
  • Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce babu wanda ya ji bakin jam'iyyar da ake binciken waɗansu manyan ƙasar nan
  • EFCC ta ce tana binciken ’yan siyasa daga dukkanin jam’iyyun siyasa, ba wai a kan adawa kawai ta tsaya ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta yi raddi ga zarge-zargen da ADC ta yi mata, inda ta ce jam'iyya ce ke ƙoƙarin siyasantar da binciken da ta ke.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, hukumar ta bayyana zargin ADC a matsayin abin mamaki da kuma wani nau’i na neman ɗora mata laifi.

Kara karanta wannan

Tsare Tambuwal ya fusata jam'iyyar ADC, ta fayyace shirin hukumar EFCC

Shugaban EFCC, Ola Olukayode, Sakataren yaɗa labaran ADC, Bolaji Abdullahi
EFCC ta yi martani ga ADC Hoto: @OfficialEFCC, @BolajiADC
Asali: Twitter

A saƙon da EFCC ta wallafa a shafinta na X, Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya yi zargin cewa jam’iyyar adawar na son kawo cikas a binciken da ta ke yi yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin shugaban EFCC ga jam'iyyar ADC

Olukoyede ya ƙaryata ikirarin ADC cewa gayyatar da EFCC ta yi wa wasu fitattun ’yan adawa a baya-bayan nan ya dogara ne kan tsofaffin shari’o’i da kuma dalilan siyasa.

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa
EFCC ta musanta son kai a bincikenta Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Ya ce:

“Babu iyaka ga lokacin da ake binciken laifuffuka. Zamba zamba ce, rashawa rashawa ce. Babu wanda ya fi ƙarfi doka. Babu abin da zai sa wanda bai aikata laifi ba ya amsa tuhuma daga EFCC.”

Olukoyede ya jaddada cewa aikin binciken EFCC na shafar ’yan siyasa daga dukkanin jam’iyyun ƙasar, yana misalta binciken da ake yi kan gwamnonin jihohi, ministoci, da manyan jami’an jam’iyya mai mulki.

Hukumar EFCC ta caccaki ADC

Shugaban EFCC ya ce bai fuskanci suka ba lokacin da yake binciken masu rike da mukaman gwamnati, don haka bai dace a soki hukumar saboda binciken ’yan adawa ba.

Kara karanta wannan

ADC ta taso APC a gaba, ta fallasa makircin da ake shiryawa 'yan adawa

Ya kara da cewa bayanan kotu sun nuna ’yan siyasa daga kowace jam’iyya na fuskantar shari’a kan tuhumar laifuffukan wadaka da tattalin arziki.

Ya ce:

“Yawancin gwamnoni masu ci daga jam’iyyun siyasa daban-daban suna fuskantar binciken EFCC."
"Ba za mu bari a yi mana barazana ko kuma mu bayyana cikakken bayani kan binciken da ake yi ba, duk irin tayar da hankali da za a yi.”

Olukoyede ya ce hukumar na aiki ne don ƴan Najeriya, domin kudin harajin da su ke biya ne ke tafiyar da ita.

Ya bukaci jam’iyyun siyasa da su maida hankali kan harkokinsu na jam’iyya, su kuma daina hana EFCC aiwatar da aikinta na kundin tsarin mulki.

Jami'an EFCC sun saki Aminu Tambuwal

A baya, kun ji cewa Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’adi (EFCC) ta saki tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

A cewar rahotanni, Tambuwal ya amsa gayyatar hukumar ranar Litinin, inda ya isa hedkwatar EFCC da 11:16 na safe inda aka tsare shi na kwanaki biyu.

Sai dai daga baya aka tsare shi bayan rahotanni suka nuna cewa bai iya bayar da cikakkiyar amsa kan tambayoyin da aka yi masa ba, amma daga bisani an sake shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng