Katsina: Basaraken da ake Zargi da Yi wa 'Yan Ta'adda Jagora Ya Fada Komar Jami'an Tsaro

Katsina: Basaraken da ake Zargi da Yi wa 'Yan Ta'adda Jagora Ya Fada Komar Jami'an Tsaro

  • Jami'an tsaron Najeriya sun yi nasarar kama Mai Unguwar Sukutum a Kankiya, da ke jihar Katsina bisa zargin ba wa ’yan bindiga bayanai
  • Rahotanni sun ce yana sanar da bata garin 'yan ta'addan duk wani motsin jami’an tsaro da kauyukan da ba su da kariya domin su kai hari
  • Salisu Abdullahi ya shaida wa jami'an da su ka kama shi cewa da shi ake tafiya wajen yin garkuwa da mutane a sassan jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina Jami’an tsaro sun kama shugaban Mai Unguwar Sukutum da ke karamar hukumar Kankiya a jihar Katsina bisa zargin yana taimaka wa ’yan bindiga da bayanan sirri.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an cafke wanda ake zargin, bisa zargin yana tattaro bayanan da za su taimaka wajen kai wa mutane hari domin garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

Gwamnan Jihar Katsina, Umaru Dikko Radda
An kama Mai Unguwa da ake zargi da ta'addanci Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Wannan na kunshe a wani bayanin bidiyon da wanda ake zargi, Salisu Abdullahi ya yi, wanda Mai Sharhi a kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama mai Unguwa a Katsina

Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa ana zargin Mai Unguwar da bayar da bayanan motsin jami’an tsaro da kuma kauyukan da ba su da kariya ga ’yan bindiga.

Wannan ya rika ba wa miyagun mutanen daman kai hare-hare cikin sauki da kuma garkuwa da mutane da dama.

Taswirar jihar Katsina
Mai Unguwa ya yi bayanin yadda ake kai hari da shi a Katsina Hoto: Legit.ng
Source: Original

An gano cewa Salisu Abdullahi ya saba ziyarar maboyar ’yan bindigar don tabbatar da ci gaba da hulɗa da kuma tsara dabarun kai hari.

Ya kuma bayyana wa hukumomi cewa har da shi ake kai hari kauyukan da ake daukar mutanen ddomin garkuwa da su.

Ana binciken Mai Unguwa a Katsina

Hukumomi sun tabbatar da cewa wanda ake zargin yana tsare a hannunsu, kuma ana cigaba da gudanar da bincike domin gano yawan tasirinsa a cikin ayyukan ta’addanci a yankin.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun babbake yan bindiga fiye da 100 a Zamfara, an yada hotuna

Majiyoyi sun ce binciken na kokarin gano sauran mutanen da ke taimaka wa ayyukan ta'addanci a sassan Katsina, wanda hakan na dakile kokarin jami'an tsaro.

Jihar Katsina ta dade tana fama da matsalar tsaro, musamman hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun sha jan hankalin cewa rashin hadin kai daga al’umma da kuma samun bayanai daga masu rike da sarautun gargajiya na kara tsananta wannan matsala.

Jagorori sun zauna da yan ta'adda a Katsina

A wani labarin, mun wallafa cewa jagororin al'umma a jihar Katsina sun sake zama da ’yan bindiga domin rage hare-haren da ake kai wa jama'a da zummar tabbatar da zaman lafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa karamar hukumar Safana ta kulla yarjejeniya da ’yan bindiga, kamar yadda wasu kananan hukumomi irin su Jibia, Batsari da Danmusa suka riga suka yi.

Haka kuma, an amince da bai wa ’yan bindiga damar zuwa kasuwa, asibiti da shaguna domin gudanar da harkokin yau da kullum, yayin da manoma za su samu damar koma wa gonakinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng