Gwamna Abba Ya Kawo Tsarin da Zai Canza Rayuwar 'Yan Daba a Jihar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci yan daba su ajiye makamai domin kawo karshe tashe -tashen hankula da aikata laifuffuka a jihar Kano
- Abba Kabir ya yi wa tubabbun yan dabar siyasa alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tsara shirin da zai taimaka masu, su koma rayuka cikin al'umma
- Ya ce wannan shirin da gwamnatinsa ta bullo da shi na gyaran halayen yan daba ba shi da alaka da siyasa, yana mai cewa za a samar masu ayyukan da suka iya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara daukar matakan kawo karshen ta'addancin yan daba da suka addabi al'umma.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga tsofaffin ‘yan dabar da suka tuba da su daina aikata ta'addanci da duk wani nau'in tashin hankali a fadin jihar Kano.

Kara karanta wannan
Kano: Abin da hadimin Abba ya ce bayan korarsa saboda zargin hannu a belin dilan 'kwaya

Source: Twitter
Abba Kabir ya yi musu alkawarin cewa matukar suka ajiye makamai, gwamnatinsa za ta gyara su tare da mayar da su cikin al’umma, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron tattaunawa na yini ɗaya da shugabannin ƙungiyoyin matasa ƙarƙashin Shirin Safe Corridor.
Gwamna Abba ya shirya kawo karshen daban Kano
Abba Kabir, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce ya zama dole a kawo ƙarshen ɗaukar makamai don aikata dabanci ko ayyukan rashin da’a.
Kwamishinan ya kuma tabbatar wa tubabbun yan daban cewa gwamnatin Kano za ta samar masu da ayyukan yi daidai da abin da aka fahimci sun fi kwarewa a kansa.
“Za mu gyara ku tare da samar muku da wurare masu tsaro inda za ku zama masu dogaro da kai.
"Bayan haka kuma, za mu ba kowane ɗaya daga cikinku aikin da ya fi dacewa da kwarewarsa,” in ji Waiya.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle ya cika alhali muna shirin kai shi asibitin kasar waje'
Gwamnatin Kano ta fara tantance yan daba
Ibrahim Waiya ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda aka tantance a baya sun rasu, lamarin da ya sa gwamnati ta shirya sabon shirin tantancewa domin sabunta bayanai.
Ya jaddada cewa wannan shirin da aka bullo da shi ba shi da alaka da siyasa, manufarsa kawai ita ce rage ayyukan daba da sauran miyagun halaye a jihar Kano, rahoton Independent.

Source: Facebook
Wannnan taron dai ya samu halartar kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) na Kano, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, da sauran abokan aiki wajen yaki da shaye-shaye da tashin hankalin matasa.
Gwamna Abba ya kori hadimansa 2 daga aiki
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kori hadimansa biyu daga aiki saboda zargin hannu a karbo belin dilan kwayoyi da karkatar da kaya.
Gwamnan ya dauki matakin ne bayan samun sakamakon bincike da kwamitoci daban-daban su ka yi tare da alakanta su da hannu a belin Suleiman Danwawu da karkatar da tallafi.
Wannan dai na cikin matakan da Gwamna Abba ya dauka tun bayan samun hannun kwamishinan harkokin sufuri na Kano da hannu a belin Danwawu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng