Tinubu: Jam'iyyar PDP Ta Faɗi Dalilin EFCC na Kama Tambuwal

Tinubu: Jam'iyyar PDP Ta Faɗi Dalilin EFCC na Kama Tambuwal

  • Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi tir da kama tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da EFCC ta yi a ranar Litinin a Abuja
  • Jam'iyyar reshen jihar Sakkwato ta bayyana lamarin da shirin siyasa na gwamnatin APC na murkushe ‘yan adawa da rage masu tasiri a kasar nan
  • PDP ta ce Aminu Waziri Tambuwal ya yi mulkin Sakkawato cikin gaskiya da amana, saboda haka kamen da aka yi masa ba shi da tushe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Jam’iyyar PDP a jihar Sakkwato ta yi Allah-wadai da kame tsohon gwamna kuma sanata mai ci, Aminu Tambuwal, da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta yi.

Babbar jam’iyyar adawa ta bayyana wannan mataki a matsayin tuggun siyasa domin murkushe muryar ‘yan adawa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal

Aminu Waziri Tambuwal Media Office
PDP ta yi magana bayan EFCC ta kama Tambuwal Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media Office
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa EFCC ta kama tsohon gwamnan Sakkwato, Tambuwal a ranar Litinin kan zargin fitar da kuɗi ba bisa ka'ida ba a lokacin yana gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tambuwal: Jam'iyyar PDP ta yi martani ga EFCC

Jaridar PM News ta ruwaito cewa a wata PDP ta yi wa EFCC martani a sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar PDP na jihar Sakkwato, Hassan Sanyinnawal, ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Jam’iyyar ta zargi gwamnatin tarayya karkashin APC da kitsa wani shiri da zai kawo tasgaro ga ƴan adawa.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
PDP ta zargi Tinubu da amfani da EFCC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

PDP ta zargi gwamnati da kokarin razana ‘yan adawa da kuma raunana tasirinsu domin kara wa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ƙarfi.

PDP ta kwantar da hankilin magoya baya

Jam’iyyar ta dage cewa Aminu Waziri Tambuwal ya ya yi mulki da gaskiya, tare da bayyana zargin EFCC da kirkiro Binciken da ba shi da tushe ballantana Malama.

Kara karanta wannan

ADC ta taso APC a gaba, ta fallasa makircin da ake shiryawa 'yan adawa

Sanarwar ta kara da cewa:

“Wannan aiki ne na ‘yan siyasa a Sakkwato da Abuja da ke cikin tsananin bukatar bata sunan Tambuwal."

PDP ta bukaci hukumomin yaki da rashawa su kasance masu tsayawa akan gaskiya, tare da kira ga magoya bayan PDP da al’ummar Sakkwato da su kwantar da hankalinsu.

Jam'iyyar ta kara da cewa:

"Mun aminta da gaskiya da rikon amanar Tambuwal, kuma wannan ba zai girgiza mu ba."

Jam'iyyar ta shawarci magoya bayanta da su jajirce wajen tabbatar da dimokuradiyya da gaskiya a kasar nan.

Hukumar EFCC ta kama Aminu Tambuwal

A baya, mun wallafa cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ofishinta da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Hukuar ta kama tsohon gwamnan ne bisa zarginsa da cire kuɗi da yawansa ya kai Naira biliyan 180 daga banki a lokacin da ya ke jagorantar jihar Sakkwato ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun bayyana cewa cire kuɗin da tsohon gwamnan ya yi ya saba wa dokar yaki da safarar kuɗi da halasta kudin haram ta shekarar 2022, sai dai har yanzu ana dakon bayanin EFCC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng